Daga cikin sauye-sauyen da ake shirin yi akwai samar da rance mai ƙarancin ruwa, ware kashi 30% na kwangilolin gwamnati ga ƙananan 'yan kasuwa, da kuma cire sharadin shekaru daga wasu shirye-shiryen tallafin gwamnati.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa za a gabatar da rahoton ga manyan masu ruwa da tsaki a jihar domin kowa ya bayar da gudunmawarsa wajen gina zaman lafiya.
A cewarsa, gwamnatin tarayya na inganta hanyoyin isar da wutar lantarki tare da haɗin gwiwar kamfanin Siemens domin samar da wutar lantarki mai ƙarfi ga masana'antu.
Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.