Sinadaran da ake amfani da su wajen nuna ‘ya’yan itatuwa na iya jefa lafiyarmu cikin haɗari – Osinbajo ya gargadi bayan matarsa ta kamu da matsanancin ciwon kai daga shan Lemu
Daga Wakiliya
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi gargadin cewa amfani da wasu sinadarai wajen noma, nuna da nika wa ‘ya’yan itatuwa da kuma adana su na iya jefa lafiyar jama’a cikin haɗari.
Osinbajo ya bayyana cewa matarsa, Dolapo, ta fara yawan fama da ciwon kai bayan ta koma shan ruwan lemu (fresh Orange juice) kullum wanda aka matse a gida.
Ya ce tun bayan da ta daina shan abubuwan sha masu ɗauke da sinadarin gas, ta koma shan babban kofi na ruwan lemu da aka matse a kowace rana.
Sai dai bayan wani lokaci ta fara samun wasu ciwon kai da ba ta saba yi ba.
Osinbajo ya ce bayan sun binciki abincin da take ci da abubuwan da take sha ba tare da gano abin da ke haddasa ciwon kan ba, sai ta aika da samfurin ruwan lemun zuwa dakin gwaje-gwaje domin a yi masa bincike.
Ya ce sakamakon binciken ya nuna cewa ruwan lemun da aka matse mata tana sha kwata-kwata bai dace da amfanin ɗan Adam ba (bai kamata mutane na shan lemun ba).
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wani taron masu aikin lambu da aka gudanar a Legas ranar 28 ga Agusta, mai taken “Leaving the Earth Better Than We Found It”.
Osinbajo ya ce sakamakon binciken ya sa suka fara tunanin cewa sinadaran da ake amfani da su wajen noman ko kuma adana ‘ya’yan itatuwa na iya zama sanadin matsalar.
Ya ce wasu manoma na amfani da magungunan kashe ƙwari masu haɗari, yayin da wasu masu sayar da ‘ya’yan itatuwa ke amfani da sinadarai wajen sa ƴaƴan itatuwa su nuna ko kuma tsawaita lokacin da za su lalace.
Ya ambaci calcium carbide a matsayin wani sinadari da ake amfani da shi wajen tilasta wasu ‘ya’yan itatuwa, kamar ayaba, mangwaro, gwanda da tumatir, su nuna cikin gaggawa.
Osinbajo ya kuma ce wani bincike da aka gudanar a Ado-Ekiti a shekarar 2024 ya nuna cewa rabin cikin ‘yan kasuwar ‘ya’yan itatuwa 20 da aka yi wa tambayoyi sun amince cewa suna amfani da calcium carbide wajen nunar ‘ya’yan itatuwansu,
Ya ce wani bincike a Uyo, jihar Akwa Ibom, shima ya gano cewa kashi 25 cikin 100 na masu sayar da ‘ya’yan itatuwa da aka tambaya sun amince da amfani da sinadarin.
Haka kuma, ya ce wani bincike da aka gudanar a Legas a 2023 ya nuna cewa 22 daga cikin masu sayar da ‘ya’yan itatuwa 50 da aka yi wa tambayoyi sun amince cewa suna amfani da wasu sinadarai wajen adana kayan amfanin gona.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kira da a ƙara tsaurara dokokin kula da lafiyar abinci tare da wayar da kan jama’a da kuma inganta hanyoyin noma da adana kayan abinci.
Ya kuma shawarci masu amfani da abinci da su kasance masu taka-tsantsan game da yadda ake noma, sarrafawa da kuma adana kayan amfanin gona kafin su kai ga teburinsu.




