Rahotanni

Za a gina layin dogo da zai haɗa jihohin Kudu maso Yamma, ya riƙa jigilar fasinjoji da kaya

Ya kuma ce hukumar na duba wasu manyan ayyukan more rayuwa, ciki har da samar da wadataccen makamashi da inganta tsarin sufuri ta tituna a yankin.

Ma’aikatan Gwamnati sun nemi Tinubu ya dawo da tallafin man fetur saboda tsadar rayuwa

Ma’aikatan Gwamnati sun nemi Tinubu ya dawo da tallafin man fetur saboda tsadar rayuwa Daga Wakiliya  Gamayyar Haɗakar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dawo da tallafin man fetur, tare da samar da wani alawus na dindindin na tsadar rayuwa (COLA) ga ma’aikatan tarayya domin rage musu radadin hauhawar farashin kayayyaki. Kiran na kunshe ne cikin wata takardar bukatu mai taken “Federal Workers Charter of Demands”, wadda mai gudanar da kungiyar, Andrew Emelieze, ya sanya wa hannu. Ma’aikatan sun kuma bukaci gwamnati ta fara biyan kashi 40 na alawus na musamman da kuma duk basussukan da suka taso tun bayan fara aiki da sabon mafi ƙarancin albashi a watan Yulin 2024. Sun kuma nemi a biya ma’aikata sauran basussukan albashi, musamman na ƙarin girma da aka samu, tare da biyan dukkan bashin fansho da wadanda suka yi ritaya suke bin gwamnati. Kungiyar ta kuma bukaci gwamnati ta samar da tsarin tallafin iyalai ga ma’aikata, inshorar lafiya ga ma’aikata da ‘yan fansho, da kuma rage harajin da ake cirewa daga alawus-alawus. Haka kuma, sun nemi gwamnati ta dauki matakan rage farashin kayan masarufi, musamman siminti, ta hanyar kara samar da kayayyakin bukatun yau da kullum a cikin gida domin samar da ayyukan yi. A bangaren jin dadin jama’a, ma’aikatan sun nemi a samar da tsarin tallafi ga marasa aikin yi da masu karamin karfi, tare da samar da kulawar lafiya kyauta ga yara, mata masu juna biyu da tsofaffi a asibitocin gwamnati. Sun kuma yi kira ga gwamnati da ta kawo karshen matsalar tsaro tare da tabbatar da sakin mutanen da aka sace a fadin kasar. Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta cire tallafin man fetur ne a ranar 29 ga Mayun 2023, lamarin da ya jawo karin farashin man fetur da kuma tashin farashin sufuri da sauran kayayyaki.

Duk Ɗan Arewa Bai Kamata Ya Ji Daɗin Kalaman Christopher Musa Ba

Duk Ɗan Arewa Mai Hankali Da Hangen Nesa Bai Kamata Ya Ji Daɗin Kalaman Ministan Tsaro Christopher Musa A Kan El-Rufa'i Ba

Matar Osinbajo ta kamu da matsanancin ciwon kai daga shan Lemu

Ya ambaci calcium carbide a matsayin wani sinadari da ake amfani da shi wajen tilasta wasu 'ya'yan itatuwa, kamar ayaba, mangwaro, gwanda da tumatir, su nuna cikin gaggawa.

ICPC ta kori jami’inta kan taimaka wa matar El-Rufai shiga wajensa ba tare da izini ba

A cikin jawabin karbar laifi da ya rubuta da hannunsa a gaban kwamitin bincike, jami’in ya ce ya ɗauki Assabe da mota zuwa harabar hukumar, sannan ya bi da ita ta ƙofar baya zuwa benen da ake tsare da El-Rufai.

FBI ta tabbatar wa kotun Amurka cewa Tinubu na cikin mutanen da aka bincika kan fataucin miyagun ƙwayoyi a 1990s

Wasu daga cikin bayanan binciken har yanzu ba a bayyana su ga jama'a ba, yayin da ake ci gaba da takaddama kan ko ya kamata a fitar da ƙarin bayanan.

Ba ko kaza da ta rage’ -‘yar gudun hijira ta ba da labarin ta’addancin ’yan bindiga a Zamfara

A cewar rahoton BBC, Fatima na daga cikin kimanin mutane 800,000 da rikicin ya raba da muhallansu a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ana dab da kammala wata sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai karfin 40MW a Lagos 

Elektron Energy ta kuma gayyaci kamfanonin da ke Victoria Island da ke sha'awar samun wutar daga tashar da su yi rajistar nuna sha'awarsu kafin a kaddamar da aikin.

Masu garkuwa sun karɓi kusan dala miliyan 5.8 a Najeriya – SBM Intelligence

Rahoton ya ce an sace mutane akalla 7,825 tsakanin watan Yulin 2025 zuwa Yunin 2026, adadin da ya karu da kashi 66 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Hare-haren ’yan bindiga ya kashe mutane fiye da 10,000 cikin shekaru biyu na gwamnatin Tinubu – Amnesty

Amnesty ta ƙara da cewa ɗaruruwan ƙauyuka sun fuskanci hare-hare tare da tilasta wa mazauna barin gidajensu a jihohin Benue, Borno, Katsina, Sokoto, Plateau da Zamfara.
- Advertisement -spot_img

DA DUMI-DUMI

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img