Za a gina layin dogo da zai haɗa jihohin Kudu maso Yamma, ya riƙa jigilar fasinjoji da kaya

DA DUMI-DUMI

Za a gina layin dogo da zai haɗa jihohin Kudu maso Yamma, ya riƙa jigilar fasinjoji da kaya

Daga Wakiliya

Hukumar Raya Yankin Kudu maso Yammacin Najeriya (SWDC) ta ce ta samu lasisin kafa layin dogo (jirgin kasa) na jigilar fasinjoji da kaya da zai haɗa jihohin yankin guda shida.

Manajan Daraktan hukumar, Dakta Charles Akinola, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da nufin tsara dabarun raya yankin da masu ruwa da tsaki suka gudanar a Cocoa House da ke Ibadan.

Ya ce hukumar za ta yi aiki tare da kamfanin Odu’a Investment Company Ltd. da kuma DAWN Commission, domin samar da tsarin layin dogo da zai haɗa sassan Kudu maso Yamma domin jigilar fasinjoji da kaya.

Ya kuma ce hukumar na duba wasu manyan ayyukan more rayuwa, ciki har da samar da wadataccen makamashi da inganta tsarin sufuri ta tituna a yankin.

Akinola ya ce akwai shirin gina wata hanya da za ta haɗa Ore a Jihar Ondo da babbar hanyar Lagos-Calabar Coastal Highway, domin samar da ingantaccen tsarin sufuri da kuma buɗe wasu sassan yankin ga ci gaban tattalin arziki.

Haka kuma, ya ce ana duba yiwuwar kafa Asusun Raya Ababen More Rayuwa na Kudu maso Yamma, wanda zai taimaka wajen ƙara kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke warewa domin ayyukan raya yankin.

Jihohin Kudu maso Yamma su ne Lagos, Ogun, Oyo, Osun, Ondo da Ekiti.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img