Burkina Faso ta hana yan kasarta fita karatu ƙasashen waje barkatai

DA DUMI-DUMI


Daga Wakiliya


Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da cewa daga yanzu duk ɗaliban da ke son ci gaba da karatun jami’a a ƙasashen waje dole ne su fara samun amincewar Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi kafin su tafi.

Gwamnatin ta ce sabon matakin zai taimaka wajen tabbatar da cewa fannonin karatun da ɗalibai za su yi sun dace da buƙatun ci gaban ƙasar, tare da sauƙaƙa musu samun aikin yi bayan sun dawo gida.

Sabuwar dokar ta shafi duk ɗaliban Burkina Faso, ko da kuwa suna samun tallafin gwamnati, na masu zaman kansu ko kuma suna ɗaukar nauyin kansu.

Matakin na zuwa ne bayan wasu sauye-sauye da gwamnatin mulkin soja ta aiwatar a fannin ilimi, ciki har da shirin horas da sabbin ɗalibai kan kishin ƙasa da kuma dakatar da ƙungiyar ɗalibai ta UGEB.

Sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun nuna damuwa cewa irin waɗannan matakai na iya ƙara takaita ‘yancin jama’a da kuma ‘yancin ɗalibai a ƙasar.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img