Dangote ya ce hannun jarin matatar sa na iya kaiwa Naira 10,000 a nan gaba

DA DUMI-DUMI

Dangote ya ce hannun jarin matatar sa na iya kaiwa Naira 10,000 a nan gaba

Daga Wakiliya

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce hannun jarin matatar man fetur ta Dangote, wanda ake sayarwa kan Naira 525 a yanzu, na iya kaiwa Naira 10,000 a nan gaba.

Attajirin ya bayyana hakan ne a wata hira da Abis Fulani, inda ya yi kira ga ƙananan masu zuba jari da su yi la’akari da sayen hannun jarin kamfanin.

Ya ce idan mutum ya zuba Naira miliyan biyar a hannun jarin, kuma farashinsa ya kai Naira 10,000, jarin nasa zai iya ƙaruwa zuwa sama da Naira miliyan 50.

“Hannun jarin yanzu Naira 525 ne. Wata rana wannan hannun jarin zai zama Naira 10,000,” in ji Dangote.

Ya ƙara da cewa masu hannun jari za su iya samun riba ta hanyar rabon kuɗin shiga, wato dividend, kuma za su iya zaɓar karɓar ribarsu a farashin Naira ko dalar Amurka don haka babu fargabar karyewar darajar Naira

Dangote ya kuma ce ƙananan masu zuba jari da ke son sayen hannun jari da Naira 50,000 ko Naira 100,000 za su samu damar yin hakan bayan kammala shiga tsarin

Sai dai, ƙimar hannun jari na iya tashi ko ta faɗi, kuma hasashen cewa zai kai Naira 10,000 ba ya zama tabbacin cewa hakan zai faru.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img