Zanga-zangar ta samo asali ne bayan rushewar rumfar tashar jirgin ƙasa a birnin Novi Sad a watan Nuwamban 2024, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 16
Darasi: Ci gaban ƙasa ba ya ta'allaka da albarkatun ƙasa kaɗai. Kyakkyawan tsari, ilimi, aiki tukuru da manufofi masu ɗorewa na iya sauya makomar kowace ƙasa.
Kamfanin Air Canada ya ce mataimakin matuƙin jirgin ne ya karɓi ragamar sarrafa jirgin tare da karkatar da shi zuwa Boston, inda aka sauka lafiya da fasinjoji 61 da ke cikinsa.
Majiyoyi sun ce matakin nata ya biyo bayan rikicin cikin gida da ya ɓarke a ƙungiyar, wacce aka kafa domin yaɗa manufofin jam'iyyar APC da kuma goyon bayan Tinubu a Arewacin Najeriya.
Tunji-Ojo ya bayyana cewa wannan ci gaba wani muhimmin mataki ne na cika burin gwamnatin Shugaba Tinubu na gina tattalin arzikin Najeriya da darajarsa za ta kai dala tiriliyan ɗaya.
Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.