Daga Wakiliya
Shekara 20 kenan tun bayan da aka gudanar da ƙidayar jama’a ta ƙarshe a Najeriya a shekarar 2006. Duk da cewa yawan jama’ar ƙasar ya ƙaru sosai, har yanzu gwamnati na amfani da ƙiyasin alkaluma wajen tsara manufofi da ayyukan ci gaba.
Ƙidayar jama’a na da matuƙar muhimmanci domin ita ce ke taimakawa gwamnati sanin adadin makarantu, asibitoci, gidaje, hanyoyi da sauran abubuwan more rayuwa da ake buƙata a faɗin ƙasar.
Sai dai, matsalolin tsaro, ƙarancin kuɗi, shirye-shiryen gudanarwa da kuma siyasa sun sa aka ci gaba da jinkirta gudanar da ƙidayar.
A zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, gwamnatin tarayya ta amince da kashe kusan Naira biliyan 800 domin shirye-shiryen ƙidayar. An ce an saki kusan Naira biliyan 224, kuma sama da Naira biliyan 200 an riga an kashe wajen sayen na’urorin zamani da sauran shirye-shiryen gudanar da aikin.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta gudanar da sahihiyar ƙidayar jama’a, yana mai cewa ingantattun bayanan jama’a na da matuƙar muhimmanci wajen ci gaban ƙasa da tsara manufofi.
Sabon shugaban Hukumar Ƙidayar Jama’a (NPC), Dakta Aminu Yusuf, shi ma ya ce hukumar ta kammala kusan dukkan shirye-shiryen gudanar da ƙidayar ta amfani da fasahar zamani, kuma tana jiran shugaban ƙasa ne kawai ya ayyana ranar gudanar da ita.
Sai dai yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa, masana na nuna damuwa cewa ci gaba da jinkirta ƙidayar na iya ƙara wahalar da gwamnati wajen tsara tattalin arziki, ilimi, lafiya, gidaje da sauran ayyukan raya ƙasa.
Ko da yake Najeriya na iya gudanar da zaɓe ba tare da sabuwar ƙidayar jama’a ba, masana sun ce ci gaba da yanke manyan shawarwari ba tare da sahihan bayanan yawan jama’a ba na iya kawo cikas ga ingantaccen tsare-tsare da ci gaban ƙasa.
Bayan shekara 20 ba tare da ƙidayar jama’a ba, tambayar da ke ci gaba da tasowa ita ce: Har yaushe Najeriya za ta ci gaba da tsara makomarta ba tare da sanin ainihin yawan mutanenta ba?





