Arewa ce tushen matsalar tsaron Najeriya amma mun ƙi fuskantar gaskiya – Shehu Sani
Daga Wakiliya
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce matsalolin ƴan bindiga da ta’addancin Boko Haram da ke addabar Najeriya sun samo asali ne daga yankunan Arewa, kafin daga bisani su yaɗu zuwa sauran sassan ƙasar da wasu ƙasashe makwabta.
A wani bayani da ya wallafa, Shehu Sani ya ce ayyukan ƴan bindiga da ƙungiyoyin ta’addanci sun janyo zubar da jinin fararen hula, sace yara, fyade, karɓar kuɗin fansa da kuma ƙona ƙauyuka.
Ya ce ƙasashen Chadi, Kamaru da Nijar ma na ci gaba da fama da matsalar tsaron da ta samo asali daga yankin.
“Ƴan bindiga da ƴan ta’adda, da yawancinsu daga yankinmu suke, suna zubar da jinin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba,” in ji shi.»
Shehu Sani ya ce a maimakon a duba yadda matsalar ta samo asali da kuma rawar da shugabannin da suka gabata suka taka wajen magance ta, ana ta ɗora alhakin matsalar kan gwamnatocin da ke kan mulki.
Ya ce an taɓa ɗora wa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan alhakin matsalar, sannan aka yi wa gwamnatin Muhammadu Buhari rangwame, yayin da yanzu ake zargin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da gazawa wajen magance matsalar.
A cewarsa, Yan Najeriya na neman abin da ya kira “mu’ujiza ko karama ta farat daya” daga gwamnatin yanzu, alhali waɗanda suka taɓa riƙe madafun iko a baya ba su samu nasarar kawo ƙarshen matsalar ba.
Shehu Sani ya kuma ce mutane basa son tuna cewa a wani lokaci a baya manyan shugabannin tsaro da tsaron ƙasar duk daga Arewa suke, inda ya ce sun karɓi ƙasar tana fama da ƴan bindiga, amma suka bar ta da matsalar da ta ƙara tsananta.
Ya ce abin takaici shi ne, ana nuna fushi ga waɗanda ake gani a matsayin “yan mowa” maimakon a tambayi shugabannin da suka fito daga yankin da kuma waɗanda suka gaza dakile matsalar tun farko sai ana neman “waɗanda za a dorawa alhaki a Zage su”
“Ba ma fushi da ƴan bindiga da ƴan ta’adda. Ba ma fushi da namu mutanen da suka gaza magance cutar. Fushinmu yana kan waɗanda muka mayar da su abin zargi da kuma duk wanda ba namu ba,” in ji Shehu Sani.
Ya kwatanta halin da yankin yake ciki da marasa lafiya da ke neman a yi musu magani, amma a lokaci guda suke ƙin karɓar sakamakon gwaje-gwajen da likitoci suka yi.
A cewarsa, al’umma na son ta rubuta nata “sakamakon gwaji” maimakon ta fuskanci gaskiyar matsalar.
Shehu Sani ya ce matsalar tsaro ta daɗe tana ci wa al’ummomin Arewa tuwo a ƙwarya, don haka bai kamata a ci gaba da neman waɗanda za a ɗora wa alhaki kawai ba, ba tare da duba tarihin yadda matsalar ta samo asali da kuma gazawar shugabannin da suka gabata wajen magance ta ba.




