Kafin Ka Kare Maganar Kosai da Kuli-kuli, da Masara …Ka Karanta Wannan

Daga Wakiliya

Maganar da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kan kosai, masara da kuli-kuli ta jawo cece-kuce a Najeriya. Wasu sun kare ta, suna cewa babu kunya a cikin yin sana’a, kuma mutane da dama sun fara rayuwarsu da ƙananan sana’o’i kafin su yi nasara. Wannan gaskiya ne.

Babu laifi ko kaɗan a sayar da kosai, gasa masara, yin kuli-kuli ko wata sana’a ta halal. Dubban iyalai sun gina rayuwarsu, sun biya wa ‘ya’yansu kudin karatu kuma sun samu ci gaba ta irin waɗannan sana’o’i. Duk aikin halal abin girmamawa ne.

Amma wannan ba shi ne abin da ya fusata ‘yan Najeriya ba.

Abin da ya fi damun mutane shi ne yadda ake ta gaya musu su ci gaba da jure wahala, alhali masu mulki suna rayuwa cikin walwala.

Idan tattalin arziƙin ƙasa yana tafiya yadda ya kamata, mutane za su yi magana ne kan sabbin damar kasuwanci, ayyukan yi, ilimi, lafiya, wutar lantarki da ci gaba.

Amma idan rayuwa ta yi tsanani, duk wata magana da ta shafi talauci tana zama abin cece-kuce.

Hakika, N50,000 na iya taimaka wa wasu ƙananan ‘yan kasuwa su ƙara jari. Amma akwai tambaya mai muhimmanci:

Yaya miliyoyin ‘yan Najeriya da ke cikin bashi, ba su da abin da za su ci, suna fama da kuɗin haya, sufuri, kuɗin makaranta da tsadar abinci?

Idan ana bin mutum bashin fiye da dubu N150,000, kuma yana fama da yunwa, shin dubu N50,000 zai warware matsalarsa?

Matsalar ba tallafin ba ce.

Matsalar ita ce jefa wa mutane talauci har ta kai ga hannu baka hannu kwarya kawai ake nuna wa a matsayin ci gaban tattalin arziƙi.

Abin da ‘yan Najeriya suke so ba rabon tallafi ba ne har abada.

Suna son tattalin arziƙin da yake aiki.

Suna son:

– Wutar lantarki mai ɗorewa domin kasuwanci ya bunƙasa.
– Abinci mai sauƙin samu.
– Tsaro domin manoma su koma gonakinsu.
– Ayyukan yi masu albashi mai kyau.
– Rancen kuɗi cikin sauƙi da sharudda masu kyau.
– Ƙasar da matasa za su iya yin mafarkin rayuwa mai kyau, ba rayuwar neman abin da za a ci kawai ba.

Abin da ya sa mutane da yawa suka fusata da maganar kosai ba saboda raina sana’ar kosai ba ne.

Saboda gajiya ce.

Saboda takaicin rayuwa.

Saboda mutane suna ganin ana ƙara ɗora musu wahala, amma ana rage musu buri.

Babu wanda ya ce ƙananan sana’o’i ba su da amfani.

Babu wanda ya ce a ji kunyar fara rayuwa daga ƙasa.

Abin da ‘yan Najeriya suke cewa shi ne:

A daina amfani da talauci a matsayin abin da za a saba da shi.

A daina nuna wahala kamar al’ada ce.

A daina ɗaukar rayuwar talauci a matsayin nasara.

A gina tattalin arziƙin da mutane za su sayar da kosai saboda sun zaɓa, ba saboda babu wata dama ba.

Ci gaban ƙasa ba auna shi ake yi da yadda mutane ke iya jure wahala ba.

Ana aunawa ne da yadda rayuwar jama’a take inganta, da yadda mutane ba sa fama da wahalar rayuwa kullum.

Wannan ce tattaunawar da ya kamata Najeriya ta mayar da hankali a kai.

‘Yan Najeriya sun cancanci fiye da rayuwar hannu baka hannu kwarya kawai.

Sun cancanci gwamnatin da za ta samar da dama, ta kare rayuka, ta bunƙasa kasuwanci, ta kuma dawo da bege ga jama’a.

Fassarar makalar : Odewale Adesoye (Green Man) daga Wakiliya

DA DUMI-DUMI

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 – Nentawe Yilwatda

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 Daga Kan Shugaban Kasa Har Kansila - Nentawe Yilwatda

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Kanun Labarai

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Sanar da Ita Cewa Zai Auri Wata — Rundunar 'Yan Sanda

Mata Sun Fi Maza Cika Alƙawarin Biyan Bashi – Inji Rahoton Moniepoint

Moniepoint ta ce alkaluman sun nuna cewa, duk da matsalolin da mata ke fuskanta wajen samun rance saboda buƙatar jingina ko rashin tarihin bashi, suna daga cikin rukunin masu kasuwanci da suka fi nuna amana wajen biyan bashin da suka karɓa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img