Al-Ajabi

Wani Magidanci ya nemi Kotu ta raba aurensa da matarsa saboda tana zuba ruwa kan gadon idan ya nemi saduwa da ita

Alkalin kotun, Chief Ademola Odunade, ya ce bayan duba lamarin, ya amince da bukatar Dauda tare da rusa auren nasu.

Kirista ya shiga Gasar Karatun Alƙur’ani a Masar, ya ci kyautar Umrah ya bai wa maƙwabciyarsa Musulma

Um Ali ta bayyana farin cikinta, inda Mina ya ce ya gan ta tana share hawayen farin ciki bayan ya sanar da ita cewa za ta samu damar zuwa Umrah.

An cire wa wani mutum dutse mai nauyin kilogiram 3.1 daga mafitsararsa a Sri Lanka

Duwatsu a mafitsara na samuwa ne lokacin da fitsari ya dade yana zama a cikin mafitsara, lamarin da ke sa wasu sinadarai da ke cikinsa su taru su zama dutse.

Kocin Masar ya suma yayin da yake ƙoƙarin raba faɗa tsakanin matansa, daga bisani ya saki uwargidarsa

Hossam Hassan, tsohon ɗan wasan tawagar ƙasar Masar ne kuma wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a tarihin ƙasar. Ya fara horar da tawagar ƙasar a shekarar 2024.

Fitaccen Jarumin Fim Nicolas Cage Ya Ce Yana Iya Tuna Abin da Ya Faru Tun Yana Cikin Mahaifiyarsa

Masana kimiyya sun ce yawancin mutane ba sa iya tuna abubuwan da suka faru kafin su kai kusan shekara biyu ko uku

An kama wata Amarya bisa zargin sanya wa mijinta guba kwana 40 da aurensu a Bauchi

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 12 ga watan Agustan 2026, da misalin karfe 3:15 na rana a kauyen Gwamma da ke karamar hukumar Bauchi.

An kama ɗa da tsohuwar matar babansa kan zargin shirya kashe mahaifinshi kuma tsohon mijinta a Kano

Sai dai kwatsam sai aka ga Alhaji ya bayyana wajen jana'izar tasa tare da jami'an tsaro, abin da ya kai ga kama ɗan nasa da tsohuwar matar tashi.

Matar da ta shafe shekaru tana ƙaurace wa nama sai ganyayyaki ta fashe da kuka bayan ta ci nama karo na farko

Soo a wani dogon bidiyo ta bayyana cewa dalilin da ya sa ta fara cin abinci marar nama ba wai kawai saboda kare dabbobi ko muhalli ba ne. Ta bayyana cewa tsawon shekaru tana kokarin rage kiba, kuma daga bisani tsarin vegan ya koma wani nau'in takura wa kanta wajen cin abinci saboda yadda take kallon jikinta.

Labarin Matashin da Ya Shafe Fiye da Shekara Takwas Yana Zaune Cikin Kogon Itacen Kuka a Yobe

Labarin Matashin da Ya Shafe Fiye da Shekara Takwas Yana Zaune Cikin Kogon Itacen Kuka a Yobe Wani matashi mai suna Muhammadu daga ƙauyen Gudi da ke ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe ya ce ya shafe kusan shekara takwas yana zaune a cikin kogon wani tsohon itacen kuka, bayan ya bar rayuwa a cikin al'ummarsa. A wata hira da ya yi, Muhammadu ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne domin samun kwanciyar hankali, saboda a cewarsa mutane a ƙauyensu ba sa fahimtarsa. Ya ce Allah ya ba shi damar ganin wasu abubuwan da ka iya faruwa nan gaba ta hanyar mafarkai. Sai dai duk lokacin da ya gaya wa mutanen ƙauyen abin da ya gani, sukan ɗauke shi a matsayin mai tabin hankali. Muhammadu ya ƙara da cewa sau da dama abubuwan da ya faɗa sun kan faru daga baya, amma duk da haka hakan bai sa mutanen ƙauyen sun canja ra'ayinsu a kansa ba. Saboda haka, ya ce ya yanke shawarar barin zama tare da jama'a, inda ya koma cikin kogon itacen kuka, wanda ya ce a nan ne yake rayuwa tun kusan shekara takwas da suka gabata. BBC ba ta da wata hujja mai zaman kanta da ke tabbatar da iƙirarin da Muhammadu ya yi na cewa yana hangen abubuwan da za su faru ta hanyar mafarkai.

An kama wani mutum a Birtaniya bayan ya hau rufin asibiti sanye da kayan “Mutuwa”, yana tsorata marasa lafiya

An kama wani mutum a Birtaniya bayan ya hau rufin asibiti sanye da kayan "Mutuwa" yana tsorata Mutane

An kama manajan makabarta da mai haƙa kabari kan zargin tono gawar mamaci domin satar akwatin gawa da nufin sayarwa

wani jami'in ƙungiyar sintiri ta sa-kai ne ya hango wasu maza biyu suna ɗauke da akwatin gawa a kan babur marar rajista, lamarin da ya sa ya tare su.