Dariye ya miƙa wa Mutfwang rahoton yadda za a samu zaman lafiya da kawo ƙarshen kashe-kashe a Filato

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Tsohon gwamnan Jihar Filato, Sanata Joshua Dariye, ya miƙa wa Gwamna Caleb Mutfwang rahoton zaman lafiya da tsaro mai kundi biyu, wanda ya ƙunshi shawarwari kan yadda za a kare al’ummomin da ke cikin haɗari, tallafa wa ‘yan gudun hijira da kuma aiwatar da gyare-gyare domin kawo ƙarshen rikice-rikicen da suka addabi jihar.

Dariye ya ce rahoton ya nuna cewa matsalolin tsaro a Filato sun samo asali ne daga dalilai masu tarin yawa, don haka ba za a iya ɗora laifin kan abu guda ba.

Ya kuma bayyana cewa an dade ana samar da rahotanni da shawarwari kan zaman lafiya a jihar, amma rashin aiwatar da su yadda ya kamata ne ya sa rikice-rikicen ke ci gaba.

A nasa bangaren, Gwamna Caleb Mutfwang ya ce rahoton zai zama jagora wajen ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Filato.

Ya ƙara da cewa Shugaba Bola Tinubu ya nuna damuwa kan halin da jihar ke ciki, tare da umartar gwamnatin jihar da ta ƙara ƙaimi wajen nemo mafita mai dorewa ga matsalar tsaro.

Gwamnan ya kuma sanar da cewa za a gabatar da rahoton ga manyan masu ruwa da tsaki a jihar domin kowa ya bayar da gudunmawarsa wajen gina zaman lafiya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img