SMEDAN ta ƙaddamar da shirin bayar da rancen miliyan 500 ga ƙananan ‘yan kasuwa ba tare da kudin ruwa ba

DA DUMI-DUMI


Daga Wakiliya


Hukumar Bunƙasa Ƙananan da Matsakaitan Masana’antu ta Najeriya (SMEDAN) ta ƙaddamar da asusun rancen Naira miliyan 500 ba tare da ruwa ba domin tallafa wa ƙananan da matsakaitan ‘yan kasuwa (MSMEs) a faɗin ƙasar nan.

Darakta Janar na SMEDAN, Charles Odii, ya bayyana hakan a Abuja yayin ganawa da ƙungiyar masu rahotannin kasuwanci da masana’antu (CICAN), a wani ɓangare na bikin Ranar MSMEs ta Duniya ta 2026.

A cewarsa, ba za a ba da rancen kai tsaye ga mutum ɗaya ba. Maimakon haka, za a rarraba kuɗin ta hannun ƙungiyoyin haɗin gwiwa (cooperatives), ƙungiyoyin sana’o’i da sauran ƙungiyoyin da aka amince da su domin tabbatar da gaskiya da sauƙaƙa dawo da rancen.

Odii ya ce an kirkiro wannan shiri ne bayan SMEDAN ta tattauna kai tsaye da ‘yan kasuwa, inda mafi yawan korafe-korafen da suka gabatar suka shafi rashin samun jari cikin sauƙi.

Ya bayyana cewa masu cin gajiyar shirin za su iya amfani da kuɗin wajen faɗaɗa kasuwancinsu, samun wurin gudanar da sana’a da kuma sayen kayan aiki.

Haka kuma, SMEDAN ta ce tana duba sabon Tsarin Manufofin MSMEs na Ƙasa, wanda za a miƙa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin amincewa da shi.

Daga cikin sauye-sauyen da ake shirin yi akwai samar da rance mai ƙarancin ruwa, ware kashi 30% na kwangilolin gwamnati ga ƙananan ‘yan kasuwa, da kuma cire sharadin shekaru daga wasu shirye-shiryen tallafin gwamnati.

Hukumar ta kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi su haɗa kai da ita wajen kafa cibiyoyin bunƙasa kasuwanci domin ƙarfafa MSMEs su ci gajiyar damar kasuwancin nahiyar Afirka ƙarƙashin yarjejeniyar AfCFTA.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img