Zamanin Amfani da Janareto a Najeriya Na Gab da Zama Tarihi -inji Ministan Wuta

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana cewa zamanin amfani da janaretocin dizal a matsayin babban tushen wutar lantarki ga masana’antun Najeriya na gab da zama tarihi, sakamakon sauye-sauyen da gwamnati ke yi a fannin wutar lantarki.

Ya bayyana hakan ne a taron makamashi na Renewable Energy Outlook Conference 2026 da Ƙungiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Legas (LCCI) ta shirya.

A cewarsa, gwamnatin tarayya na inganta hanyoyin isar da wutar lantarki tare da haɗin gwiwar kamfanin Siemens domin samar da wutar lantarki mai ƙarfi ga masana’antu.

Ministan ya ce Dokar Wutar Lantarki ta 2023 ta bai wa jihohi da kamfanoni damar samar da nasu wutar lantarki ta hanyar mini-grid da kuma haɗa kai tsaye da masu samar da wuta masu zaman kansu.

Ya ƙara da cewa matsalar ƙarancin wutar lantarki na jefa masana’antun ƙasar cikin asarar biliyoyin naira a duk shekara saboda dogaro da janaretocin dizal da fetur.

Tegbe ya ce gwamnati ta riga ta ƙara ƙarfin na’urorin canja wutar lantarki tare da jawo sama da dala biliyan biyu na jarin masu zaman kansu, yana mai cewa ana ci gaba da ɗaukar matakan da za su tabbatar da ingantacciyar wutar lantarki domin bunƙasa masana’antu da tattalin arzikin ƙasa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img