Bama yi a kai kasuwa : “Ba zan kare waɗanda suka jefa jama’a cikin wahala ba” – Matashi Murtala Provost ya ƙi karɓar naɗin da aka yi masa a kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu 2027
Daga Wakiliya
Wani matashin ɗan siyasa, Muhammad Murtala Musa D Provost, ya ƙi karɓar naɗin da aka yi masa a matsayin mamba a kwamitin yaɗa labarai (New Media) a kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu da jam’iyyar APC na 2027.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Malam Murtala ya ce ya ga sunansa cikin jerin mutanen da aka naɗa domin yin aiki a kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu na 2027.
Ya ce, duk da godiya da ya yi wa waɗanda suka ga ya cancanci wannan matsayi, ya yanke shawarar ƙin karɓar naɗin.
Murtala ya ce ba zai yi amfani da ƙarfinsa wajen kare mutanen da ya yi zargin cewa manufofinsu ne suka jefa al’umma cikin wahala ba.
“Zan yi amfani da ƙarfina wajen tallata duk wanda ya yi alkawarin dawo da tallafin man fetur idan ya ci zaɓen shugaban ƙasa na 2027, har da Shugaba Bola Tinubu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ba ya ganin ya dace ya kare mutanen da ya ce su ne suka haifar da wahalhalun da jama’a ke ciki.
Ya roƙi Allah Ya saka wa waɗanda suka yi tunanin naɗa shi da alheri, tare da yi musu fatan alheri.




