Majalisar Birtaniya ta ƙi amincewa da dokar taimaka wa masu fama da cutar ajali su mutu

DA DUMI-DUMI

Majalisar Birtaniya ta ƙi amincewa da dokar taimaka wa masu fama da cutar ajali su mutu

Daga Wakiliya

’Yan majalisar dokokin Birtaniya sun ƙi amincewa da wani kudirin doka da zai ba wasu marasa lafiya masu fama da cutar ajali damar neman taimako domin su kawo ƙarshen rayuwarsu.

A zaɓen da aka gudanar a majalisar wakilai ta ƙasar ranar Juma’a, ’yan majalisa 286 suka kada kuri’ar ƙin amincewa da kudirin, yayin da 270 suka goyi bayanta.

Kudirin, wanda ya shafi Ingila da Wales, zai bai wa manya da aka tabbatar cewa saura ƙasa da watanni shida su rayu damar zaɓar kawo ƙarshen rayuwarsu, idan suna da cikakkiyar fahimta kuma sun bayyana burinsu da kansu.

Sai dai, za a buƙaci amincewar likitoci biyu da kuma wani kwamitin ƙwararru kafin a aiwatar da hakan.

Masu yaƙin neman a amince da dokar sun bayyana matakin a matsayin koma-baya mai girma, yayin da masu adawa suka ce hakan ya kare mutanen da ka iya fuskantar matsin lamba.

Kudirin ya sake kunno kai ne bayan da irin wannan doka ta samu goyon bayan majalisar wakilai a bara, amma daga baya aka dakatar da ita a Majalisar Dattawa ta Birtaniya.

Assisted dying ya halatta a wasu ƙasashe, ciki har da Kanada da Switzerland

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

An kashe mutumin da ake zargi ya daba wa limamin Juma’a a Wuka a Sokoto

Rahotanni sun ce matashin, wanda aka bayyana da suna Mai Barewa, yana cikin masu ibadar da suka halarci sallar, kuma ya kai wa malamin hari har sau biyu.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img