2027: INEC ta ki baiwa NDC damar ɗora sunayen ‘yan takarar ta

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta ce Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ƙi ba ta lambar sirri (Access Code) da za ta yi amfani da ita wajen ɗora sunayen ‘yan takararta a shafin hukumar gabanin zaɓen 2027.

Mai magana da yawun jam’iyyar, Osa Director, ya ce sun nemi lambar daga INEC amma har yanzu ba su samu amsa ba. Ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta yanke, wanda ya umarci INEC da kada ta amince da NDC har sai an kammala shari’o’in da ke kanta.

A nata ɓangaren, shugabannin NDC sun dage cewa jam’iyyar tana nan a matsayin halastacciyar jam’iyya, kuma za ta tsaya takara a zaɓen 2027.

Shugaban jam’iyyar, Sanata Moses Cleopas Zuwoghe, ya ce hukuncin kotun bai soke rajistar NDC ba, yana mai tabbatar da cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, da sauran ‘yan takara za su kasance a takardar zaɓe idan an kammala shari’ar.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img