Ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka kafa APC ya ce sun yi kuskure, ya roƙi Allah Ya yafe musu: “Mun ƙirƙiro masifa ne ba tare da saninmu ba” – Sir Jalal Falal
Daga Wakiliya
Ɗaya daga cikin jiga-jigan matasan da suka taka rawa wajen kafa jam’iyyar APC, Sir Jalal Falal, ya nemi afuwar Allah kan rawar da ya ce sun taka wajen samar da jam’iyyar.
A wani rubutu da ya wallafa yayin da yake tsokaci kan wani tsohon rubutunsa da Facebook ya tunasar da shi, Jalal ya ce shekaru 13 da suka gabata sun kai ruwa sun kai mari wajen goyon bayan kafa APC ba tare da sanin abin da suke taimakawa wajen samarwa ba.
A ranar 7 ga Satumba 2013, Jalal ya wallafa hoton wani taro da ya halarta a Hamdala Hotel, inda ya rubuta cewa yana wajen taron kwamitin zartarwa na ƙungiyar APC National Youth Vanguard.
Yayin da Facebook ya sake tunasar da shi da wannan rubutu, Jalal ya ce: “Shekaru 13 bayan haka, mun waiwaya kan lokacin da muke goyon bayan APC, ba tare da sanin cewa muna ƙirƙirar wani dodo ba. Allah Ya yafe mana.”
Jalal, wanda a yanzu yake cikin jam’iyyar adawa, na daga cikin masu fafutukar adawa da gwamnatin APC a matakin jiha da tarayya, yayin da ake tunkarar zaɓen 2027 suna da burin kawar da APC daga sama har ƙasa.




