NNPC ta ƙaddamar da tashar mai ta farko da masu mota ke zubawa kansu a Abuja kamar yadda ake yi a wasu kasashen Turai
Daga Wakiliya
Kamfanin NNPC ya ƙaddamar da tasharsa ta farko mai amfani da fasahar zamani wajen sayar da mai kai tsaye ga abokan ciniki a Abuja.
Tashar, da ke kan titin Bill Clinton Drive, Airport Road, tana ba masu ababen hawa damar zuba wa kansu mai, tare da samun wuraren cajin motocin lantarki, sayar da iskar gas ta LPG, wankin mota da kuma gyaran ababen hawa.
Tashar mai aiki sa’o’i 24 tana amfani da makamashin hasken rana mai ƙarfin sama da kilowatt 200.
NNPC Retail ta ce abokan ciniki za su iya amfani da manhajar waya wajen biyan kuɗin mai da samar da lambar da za ta ba su damar zuba adadin da suka saya.
Kamfanin ya kuma bayyana cewa yana shirin ƙaddamar da irin waɗannan tashoshi tsakanin 50 zuwa 70 a faɗin Najeriya cikin watanni shida masu zuwa.
Shin ina da ina ya kamata a fara kaddamar da irin waɗannan gidajen mai?




