Duk Ɗan Arewa Bai Kamata Ya Ji Daɗin Kalaman Christopher Musa Ba

DA DUMI-DUMI

TSOKACI: Duk Ɗan Arewa Mai Hankali Da Hangen Nesa Bai Kamata Ya Ji Daɗin Kalaman Ministan Tsaro Christopher Musa A Kan El-Rufa’i Ba

Daga Bashir Abdullahi El-Bash

 

‎Domin kuwa kowa ya san jajircewar El-Rufa’i kan shugabanci da ba da gudunmawa wajen daƙile matsalolin tsaron Jihar Kaduna. Shi ne ya jajirce ya ce zai tada garin Gonin Gora matuƙar aka ci gaba da aikata laifukan ta’aḍḍaɲci a yankin.

‎Ban ce El-Rufa’i ba shi da laifi ba, domin dole yana da kura-kurai irin nasa a matsayinsa na ɗan’adam. Ni ina cikin masu ganin kisan kiyașhiɲ da aka yi wa ƴan Shi’a a Zaria ba daidai ba ne wanda kowa ya sani a lokacisa aka yi hakan yana gwamna.

‎Amma duba da gudunmawar da ya bayar wajen tsayuwa tsayin daka wajen kawo Tinubu da jajircewarsa kan harkar tsaro, da sauran muhimman abubuwa da ya yi a matsayin shugaba sun kai a yaba masa.

‎El-Rufa’i sai da ya yi rigima da manyan Arewa dattawa da sarakuna a ƙoƙarinsa na ganin Tinubu ya ci zaɓe. Kenan ko ba komai wannan ya isa ya sa Ministan tsaro Musa ya saurara masa a matsayinsa na minista.

‎Sannan, a matsayinsa na Ministan tsaron ƙasa bai kamata ya kasance mai haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’umma ba. Mutane da dama a Arewa suna yi masa kallon Kirișța mai sauƙin kai wanda ba zai ɗauki ɓangare ba. Wasu ma a zatonsu musulmi ne kuma ɗan Arewa saboda yadda suffarsa da dattakonsa ya nuna in banda yanzu da ya nuna kansa.

‎Saboda haka, ya kamata Christopher Musa ya zama dattijo wanda zai iya tafiya tare da kowa a Najeriya ba tare da wariyar addini ba kamar yadda muhimman mutane irin su TY Ɗanjuma da Yakubu Gawon da sauran manyan kiristoci suka yi tsawon shekaru.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

An kashe mutumin da ake zargi ya daba wa limamin Juma’a a Wuka a Sokoto

Rahotanni sun ce matashin, wanda aka bayyana da suna Mai Barewa, yana cikin masu ibadar da suka halarci sallar, kuma ya kai wa malamin hari har sau biyu.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img