An gurfanar da ma’aikaciyar jinya kan zargin damfarar marasa lafiya dala miliyan $906, ta sayi Ferrari da abin wuya na Alfarma

DA DUMI-DUMI


Daga Wakiliya


Hukumar Shari’a ta Amurka ta gurfanar da wata ma’aikaciyar jinya mai suna Mariel Yukee, mai shekaru 49, kan zargin damfarar shirin inshorar lafiya na gwamnati (Medicare) da sama da dala miliyan 906.

A cewar masu bincike, Yukee ta rika gabatar da takardun neman kuɗi na magunguna da jinyar raunuka ga tsofaffin marasa lafiya da ke kula ta ƙarshe (hospice), duk da cewa ba sa buƙatar irin wannan magani. Ana kuma zarginta da ƙirƙirar bayanan lafiya na bogi domin a amince da biyan kuɗin.

Hukumomi sun ce daga cikin kuɗin da aka nema, an biya kusan dala miliyan 297 kafin aka gano zargin damfarar.

Bincike ya nuna cewa ta yi amfani da wasu daga cikin kuɗaɗen wajen sayen motar alfarma ta Ferrari 296 GTS mai darajar kusan dala 594,000, da kuma abin wuya na Bulgari da ya kai dala 865,000.

Lamarin na daga cikin wani gagarumin samame da hukumomin Amurka suka gudanar kan damfarar harkar lafiya, inda aka gurfanar da mutane 455, ciki har da likitoci 90, bisa zargin damfarar da ta haura dala biliyan 6.5 a faɗin jihohi 45 na ƙasar.

#Wakiliya | Muryar Arewa a Duniya

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img