“Mutanena” Ko Siyasa? – Tambayoyin Da Ya Kamata Christopher Musa Ya Amsa Wa ’Yan Kudancin Kaduna Domin Su Gane Soyayya Ce Ko Kuma Neman Amfani Da Su A Siyasa

DA DUMI-DUMI

TSOKACI: “Mutanena” Ko Siyasa? – Tambayoyin Da Ya Kamata Christopher Musa Ya Amsa Wa ’Yan Kudancin Kaduna Domin Su Gane Ko Soyayya Ce Ko Kuma Neman Amfani Da Su A Siyasa

Daga Wakiliya

Duk da cewa mun yi zaton duka ’yan jihar Kaduna, har ma da dukkan ’yan Najeriya – Musulmi da Kirista – sun zama mutanen Honourable Christopher Musa, amma tunda shi da kansa ya yi amfani da kalmar “mutanena”, bari mu tsaya a nan mu yi tambaya.

Idan wannan magana ba ta da alaƙa da siyasa, kuma da gaske yana kallon ’yan Kudancin Kaduna a matsayin “mutanensa”, to ya kamata a samu abubuwan da za su tabbatar da hakan.

’Yan Kudancin Kaduna, a tsawon shekarun da Honourable Christopher Musa ya kwashe yana aikin soja, wane irin ci gaba ya kawo muku da za ku iya dubawa a yau ku ce: “Eh, wannan mutum ya nuna mana ƙauna da gaske”?

 

Ba wai kawai a ce “mutanena” ba. Me aka yi wa mutanen?

“Mutanena” Ba Kalma Kawai Ba Ce: Me Christopher Musa Ya Yi Wa Kudancin Kaduna?

Idan da gaske ne:

– Mutane nawa ya taimaka aka samar musu da tsayayyen aikin yi?

– Guda nawa ya taimaka aka tura karatu ko samun guraben ilimi?

– Guda nawa ya taimaka suka shiga aikin soja ko wasu ayyukan gwamnati?

– Mutane nawa ya taimaka aka ƙarfafa su ta hanyar jari ko tallafin kasuwanci?

– Kamfanoni ko manyan ayyukan ci gaba nawa ya yi amfani da matsayinsa da damar da ya samu wajen jawo su zuwa Kudancin Kaduna?

– Fastoci, malamai, dattawa da shugabannin al’umma nawa ya taimaka musu ko ya tsaya tare da su a lokacin da suke cikin buƙata?

– Sau nawa ya je wajen ’yan Kudancin Kaduna domin yi musu jaje a lokacin da aka kashe ’yan uwansu?

– Kuma a lokutan da aka samu kashe-kashe, wane takamaiman mataki ya ɗauka ko ya yi ƙoƙarin ɗauka domin ganin an kawo ƙarshen matsalar?

Ko kuwa yanzu ne, lokacin da ake buƙatar “mutanena” domin wata manufar siyasa, aka sake tuna wa da su?

Ba muna cewa Christopher Musa bai kamata ya ce ’yan Kudancin Kaduna mutanensa ba ne. A’a.

Tambayar ita ce: idan da gaske ne su ne mutanensa, ina shaidar wannan alaƙar a cikin shekaru?

Domin ƙaunar mutane ba ta tsaya ga kalmomi ba. Ayyuka ne ke tabbatar da ita.

Kuma idan har akwai irin waɗannan ayyukan, ya kamata ’yan Kudancin Kaduna su fito su nuna su – domin su tabbatar wa duniya cewa “mutanena” ba wata kalmar siyasa ba ce, sai dai magana ce da ke da tarihi da hujjar aiki a bayanta.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

An kashe mutumin da ake zargi ya daba wa limamin Juma’a a Wuka a Sokoto

Rahotanni sun ce matashin, wanda aka bayyana da suna Mai Barewa, yana cikin masu ibadar da suka halarci sallar, kuma ya kai wa malamin hari har sau biyu.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img