Dukan yara a matsayin horo na iya sa su fanɗare su zama mugaye idan sun girma -inji Masana

Duka a matsayin horo na iya sa yara su fanɗare su zama mugaye idan sun girma -inji Masana

Daga Wakiliya 

Wata masaniyar ilimin halayyar ɗan Adam ta ce amfani da hukunci mai tsauri, musamman duka, wajen ladabtar da yara na iya ƙara yiwuwar sakasu su zama fanɗararru masu kunnen ƙashi a nan gaba.

Dokta Liane Alampay, malamar ilimin halayyar ɗan Adam a Jami'ar Ateneo de Manila da ke Philippines, ta bayyana hakan ne a gaban wani kwamiti na Majalisar Dattawan ƙasar da ke kula da harkokin mata, yara da iyali.

Ta ce binciken da aka gudanar tsawon shekaru a ƙasashe daban-daban bai nuna cewa duka hanya ce mai inganci wajen tarbiyyar yara ba.

Maimakon haka, a cewarta, an gano alaƙa tsakanin tsauraran hanyoyin tarbiyya da yiwuwar yara su ƙara fanɗarewa su lalace yayin da suke girma.

“Ba za a iya cewa abu guda ne ke haifar da lalacewar matasa ba,” in ji ta, tana mai cewa tarbiyyar da yaro ya samu, yanayin gidansa da kuma abubuwan da ya fuskanta duk na iya yin tasiri.

Ci gaban kwakwalwa

Dokta Alampay ta kuma ce yara da matasa har yanzu suna cikin wani mataki na inganta tunani da iya sarrafa motsin zuciyarsu.

Hakan na iya sa su kasa fahimtar illar wasu matakai da suke ɗauka ko kuma su kasa sarrafa fushi yadda ya kamata.

Ta ce saboda haka, horon da ya fi mayar da hankali kan fahimtar kuskure da koyar da yaro abin da ya dace na iya zama mafi amfani fiye da hukuncin da ke jawo tsoro kawai.

A Philippines, Ma'aikatar Jinƙai da Ci gaban Jama'a tana amfani da tsarin da ya fi mayar da hankali kan gyara da sake shigar da yara da suka yi laifi cikin al'umma.

Wannan tsarin ya fi duba ci gaban yaro da gyara halayensa, maimakon dogaro da hukunci kawai.

Tsohuwar al'ada

A wurare da dama, ciki har da wasu al'ummomi, iyaye sun dade suna kallon duka a matsayin wata hanya ta koya wa yaro biyayya.

Sai dai bayanan binciken da aka gabatar wa ‘yan majalisar sun sake haifar da muhawara kan abin da ya kamata a kira ingantacciyar tarbiyya.

Tambayar ita ce: Shin manufar horo ita ce kawai yaro ya ji tsoron hukunci, ko kuwa ya fahimci kuskurensa kuma ya koyi yadda zai zama mutum mai ɗaukar nauyi?

A cewar masana, amsar wannan tambayar na iya sauya yadda iyaye ke kallon tarbiyyar yara.

DA DUMI-DUMI

Matashi ya yi bidiyo a TikTok ya yi ‘tagging’ Shugaban New York, yana korafi a gyara wasu ramuka da ya gani – kafin ya...

Matashi ya yi bidiyo a TikTok ya yi 'tagging' Shugaban New York Mamdani, yana korafi a gyara wasu manyan ramuka da ya gani – kafin ya je aiki ya dawo har an gyara

Kocin Masar ya suma yayin da yake ƙoƙarin raba faɗa tsakanin matansa, daga bisani ya saki uwargidarsa

Hossam Hassan, tsohon ɗan wasan tawagar ƙasar Masar ne kuma wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a tarihin ƙasar. Ya fara horar da tawagar ƙasar a shekarar 2024.

Da kyar Tinubu ya amince da Osinbajo a matsayin mataimakin Buhari – ya dage sai an bai wa matarsa Oluremi

Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya kuma ce lokacin da Buhari ya nemi goyon bayansa bayan taron APC na 2014, ya sharɗanta masa cewa kada ya tsaya da tikitin Musulmi da Musulmi.

Da Tinubu ya so APC ta ci zaɓen Osun ko ta halin ƙa-ƙa, da ni za a tura jihar -Wike

Ya ce: “Da Shugaban kasa na son cin zaben Osun da ko-ta-halin ƙa-ƙa, da na je can, kuma da mun ci zaben. Babu abin da gwamnan zai iya yi.”

APC ta zargi an yi mata magudin zaɓe a Osun, ta nemi a sake duba sakamakon

Sai dai APC ta ce tana ci gaba da duba sakamakon da yadda aka gudanar da zaɓen, wanda zai iya zama matakin farko na ƙalubalantar sakamakon da aka sanar.

Kanun Labarai

Wike ya umarci a rushe duk gidajen da suka toshe hanyoyin ruwa a Abuja

Wike ya umarci rushe gidajen da aka gina kan hanyoyin ruwa a Abuja Daga Wakiliya  Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya umarci hukumomin birnin da su fara rushe gidajen da aka gina ko kuma suka tare hanyoyin ruwa a Abuja. Wike ya bayar da umarnin ne bayan ya duba wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a Maitama ranar Talata. Ya ce za a fara aikin nan take kuma za ayi ta aikin har zuwa ranar Asabar, ba tare da la'akari da masu gidajen ba. Ministan ya ce wasu daga cikin gine-ginen mallakin 'yan majalisa da wasu masu hannu da shuni ne, amma doka za ta shafi kowa. Ya ce gine-gine a kan hanyoyin ruwa, toshe magudanan ruwa da zubar da shara na daga cikin abubuwan da ke haddasa ambaliyar ruwa a Abuja. Wike ya kuma umarci hukumomin FCT da su gaggauta kwashe laka da datti daga magudanan ruwa a babban birnin,  Ya ce sauyin yanayi da yawan ruwan sama na taka rawa wajen ambaliyar, amma ayyukan mutane ma na kara tsananta matsalar. Ministan ya ce ba za a dakatar da rushe-rushen saboda ana cikin lokacin siyasa ba, yana mai cewa gwamnati na da niyyar tabbatar da dokokin tsara birnin.

Daga yanzu ‘Daukar doka a hannu’ daidai yake da kisan kai — IGP Disu ya gargadi ’yan Najeriya

Ya gargadi mutanen da ke shirya ko tunzura jama'a, wadanda ke daukar hotuna ko bidiyon abin da ke faruwa su yada shi, da kuma wadanda ke hana ’yan sanda shiga tsakani ko kai agajin gaggawa kan wanda ake zargi, cewa su ma za su iya fuskantar tuhuma.

Ya Allah Ka Kare Mu Daga Maza Azzalumai – labarin wata maijego da na gani a asibiti ya girgiza ni

Ta haihu babu ko tsinke na haiuwa daga mijin, ya ki rako ta Asibiti, babu wani nashi kuma ko sisi bai bayar ba, ita ce matar shi ta huɗu, haihuwa na 11, yan uwanta suke komai, tana cikin nakuda ma sai da tayi mashi tuwo kafin ta taho Asibiti....
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img