EFCC Ta Kwato Fiye da Naira Biliyan 38.66 a Binciken Badakalar Gyaran Matatun Mai

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Hukumar EFCC ta ce ta kwato fiye da Naira biliyan 38.66, kuɗaɗe da kadarori, yayin binciken zargin karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin gyaran matatun mai na Port Harcourt, Warri da Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa an kwato Naira biliyan 9.4, da kuma dala miliyan 21.2, baya ga wasu filaye da kadarori da ake zargin an mallaka da kuɗaɗen da aka karkatar.

Ana zargin wasu tsofaffi da na yanzu daga NNPCL, shugabannin matatun mai da kuma wasu kamfanonin kwangila da hannu wajen karkatar da kuɗaɗen gyaran matatun, duk da cewa gwamnatin tarayya ta kashe kusan dala biliyan 2.8 kan aikin.

EFCC ta bayyana cewa binciken na ci gaba, kuma ana sa ran ƙarin ƙwato kadarori tare da gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img