Gurbataccen abin sha ya kashe sama da mutum 30 a Ondo, wasu fiye da 50 na asibiti

DA DUMI-DUMI

Gurbataccen abin sha ya kashe sama da mutum 30 a Ondo, wasu fiye da 50 na asibiti

Daga Wakiliya

Wani mutum da ya tsira daga shan wani gurbataccen abin sha a jihar Ondo, ya ce idan Allah ya cece shi, ba zai sake shan barasa ba.

Lamarin ya faru ne a wasu sassan ƙaramar hukumar Odigbo, inda ake zargin shan gurbatattun abubuwan sha da aka kera a gida ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 30, yayin da wasu fiye da 50 ke kwance a asibitoci.

Rahotanni sun ce mutanen da abin ya shafa sun fito ne daga Odigbo, Newtown, Orita da Araromi-Obu.

Shugaban ƙaramar hukumar Odigbo, Adegoroye Taiwo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kama wani mutum da ake zargin ya sayar da abin shan.

Ya ce an miƙa wanda ake zargin ga ‘yan sanda a Akure, yayin da ake ci gaba da bincike kan asalin abin shan.

A cewar shugaban, binciken farko da kwararrun likitoci da masana guba suka gudanar ya nuna cewa mutuwar na da alaƙa da shan gurbatattun barasa na gida, da ake kira da sunaye daban-daban kamar Jeji, Ere da Monkey Tail.

Ya ce gwamnatin jihar ta tura tawagar lafiya da ta haɗa da jami’an Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya, NAFDAC, da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.

A halin yanzu, an hana sayarwa da shan barasa da aka kera a gida a ƙaramar hukumar, tare da umartar jami’an tsaro su kama masu karya dokar.

 

Wanda ya tsira ya ba da labari

Shola Adebayo, mai shekara 32, ya ce ya fara samun matsalar gani bayan ya sha abin sha da ake kira Monkey Tail.

Ya ce ya sha ƙwarya biyu ne bayan wani abokinsa ya kawo abin shan daga Ore, amma washegari ya kasa gani yadda ya kamata.

“Ina samun sauƙi, amma ina addu’ar Allah ya ceci idona. Idan Allah ya cece ni, na rantse ba zan sake shan wani abin sha ba, har da giya,” in ji shi.

Wani ɗan’uwan wasu daga cikin waɗanda suka mutu, Adebayo Adetayo Adedeji, ya ce al’ummar ta rasa matasa uku, ciki har da ɗan uwansa da wasu abokansa.

Shi ma sarkin Odigbo, Oba Rufus Akinrimade, ya ce bincike ya nuna cewa mutuwar ba ta da alaƙa da wata haramci ta al’ada, illa shan gurbatattun barasa.

Hukumomi sun ce ana ci gaba da bincike, kuma ana jiran cikakken adadin waɗanda abin ya shafa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img