Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

DA DUMI-DUMI

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Daga Wakiliya

Gwamnatin Tarayya ta fara biyan tsoffin ma’aikatan kamfanin jiragen sama na Nigeria Airways kuɗaɗen sallama daga aiki da suka daɗe suna jira.

Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziƙi, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa gwamnati za ta biya jimillar Naira biliyan 18 ga tsoffin ma’aikata 2,700.

Ya ce zuwa yanzu an biya ma’aikata 2,100, yayin da aka amince da biyan wasu 600 da ke cikin rukuni na takwas da na tara.

Ministan ya ce ana biyan kuɗaɗen ne a rukuni-rukuni domin waɗanda aka kammala tantancewa kada su ci gaba da jira, yayin da ake tantance sauran masu neman haƙƙinsu.

Ya ƙara da cewa kuɗaɗen sun shafi ma’aikata manya da ƙanana, ba tare da bambanci ba. Ga waɗanda suka rasu kafin su karɓi haƙƙinsu, za a biya magadansu ko waɗanda doka ta amince da su bayan kammala matakan da suka dace.

Nigeria Airways ta daina aiki a shekarar 2003, kafin a kammala aikin rushe kamfanin a shekarar 2005.

Oyedele ya ce biyan kuɗaɗen ya samo asali ne daga umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa haƙƙin ma’aikatan ne, ba wata alfarma da gwamnati ta yi musu ba.

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

An kashe mutumin da ake zargi ya daba wa limamin Juma’a a Wuka a Sokoto

Rahotanni sun ce matashin, wanda aka bayyana da suna Mai Barewa, yana cikin masu ibadar da suka halarci sallar, kuma ya kai wa malamin hari har sau biyu.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img