‘Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami
Daga Wakiliya
Ɗan takarar gwamnan Gombe na jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ce yana da gungun mabiya (tsarin structure na siyasa) sama da 22,000 a faɗin jihar.
Tsohon Ministan ya ce shahararsa a ƙauyuka da garuruwan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta, yana mai cewa magoya bayansa mutane ne na gaske.
Ya kuma ce ya shiga takarar gwamna ne bayan dattawa, matasa da masu ruwa da tsaki sun matsa masa ya yi takarar, sannan ya nemi zaɓin Allah ta hanyar addu’ar Istikhara da Umrah.
Pantami ya bayyana talauci, rashin ilimi da rashin aikin yi a matsayin manyan matsalolin Gombe.
Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
Ya kuma ce ba ya tsoron binciken EFCC, yana mai cewa duk jami’in gwamnati da ya yi gaskiya bai kamata ya ji tsoron bincike ba.
Pantami ya ƙalubalanci sauran ’yan takarar gwamna, ciki har da na APC, Jamilu Gwamna, da su fito a yi muhawara kan shirye-shiryen shugabanci.




