Abubuwa 6 da ya kamata a yi kafin ƙarfe 9 na safe domin rage haɗarin shanyewar ɓarin jiki
Daga Wakiliya
Shanyewar ɓarin jiki na daga cikin matsalolin lafiya da ka iya sauya rayuwar mutum ko ma janyo mutuwa. Kuma ba lallai sai mutum ya tsufa ba kafin ya fuskance ta, domin masana sun ce ana samun ƙarin matasa da ke fuskantar matsalar.
Sai dai akwai wasu matakai da mutum zai iya ɗauka domin rage haɗarin kamuwa da shanyewar ɓarin jiki.
Ga wasu abubuwa shida da masana ke ba da shawarar a yi da safe:
1. Sha magungunan da likita ya rubuta maka
Idan kana amfani da maganin hawan jini ko rage ƙiba a jini, yana da muhimmanci ka riƙa shan maganin yadda likita ya umarta.
Masana sun ce sarrafa hawan jini na daga cikin muhimman hanyoyin rage haɗarin shanyewar ɓarin jiki.
Saboda haka, kada a riƙa mantawa ko daina shan magani ba tare da shawarar likita ba.
2. Yi addu’a, tunani ko rungumar wanda kake so
Rage damuwa na iya taimakawa wajen rage hawan jini, wanda hakan kuma zai iya rage haɗarin shanyewar ɓarin jiki.
Masana sun ce mutum zai iya yin addu’a, karanta wani abu mai ƙarfafa zuciya ko yin ƴan mintuna na nutsuwa da safe.
Haka kuma, rungumar masoyi, ɗan uwa, aboki ko ma dabba da ake kiwo na iya taimakawa wajen rage damuwa.
Idan ba ka son runguma, kiran aboki ko ɗan uwa da waya da yin hira da shi ma na iya taimakawa.
3. Ka rage amfani da kayan zaƙi na roba da zaƙi a cikin Coffee
Masana sun ce mutum na iya shan Coffee da safe matuƙar bai wuce adadin caffeine da ya dace ba.
Sai dai ana ba da shawarar a yi taka-tsantsan da wasu kayan zaƙi na roba, musamman xylitol, wanda wasu bincike suka danganta da ƙarin haɗarin samuwar daskararren jini da wasu matsalolin zuciya.
4. Ka motsa jiki
Ba dole sai ka je wajen motsa jiki na musamman ba. Za ka iya yin tafiya da kafa, hawa matakala maimakon amfani da lif, ko hawa keke idan hakan ya dace da kai.
Masana sun ce yawan zama ba tare da motsa jiki ba na iya ƙara haɗarin shanyewar ɓarin jiki.
An ba da shawarar mutum ya yi ƙoƙarin kai akalla tattaki dubu 7,000 a rana, ko fiye idan lafiyarsa ta ba shi dama.
5. Ka daina shan taba ko amfani da vape
Shan taba na daga cikin abubuwan da ke ƙara haɗarin shanyewar ɓarin jiki.
Masana sun kuma yi gargadi game da amfani da vape, domin yana da illa. A guje Vape idan ana son kare lafiyar zuciya da jijiyoyin jini.
Idan kana shan taba ko amfani da vape, daina amfani da su na daga cikin manyan matakan da za ka iya ɗauka domin rage haɗarin.
6. Ka ci abincin safe mai gina jiki
Abincin safe mai kyau na iya taimakawa wajen kula da lafiyar zuciya da jijiyoyin jini.
Masana sun ba da misalin cuku mai laushi (cottage cheese) da ‘ya'yan itatuwa kamar plum ko kankana, tare da ƙwayoyin flaxseed.
Flaxseed na ɗauke da nau'in kitse na omega-3 da kuma sinadarin fiber da ake dangantawa da inganta lafiyar jijiyoyin jini.
Sai dai ana ba da shawarar a rage abincin safe mai yawan ƙarin sukari, domin yawan sukari na iya ƙara haɗarin kamuwa da ciwon sukari, wanda shi ma na daga cikin abubuwan da ke ƙara haɗarin shanyewar ɓarin jiki.
A ƙarshe
Ƙananan sauye-sauye a rayuwar yau da kullum na iya taimakawa wajen rage haɗarin shanyewar ɓarin jiki.
Shan magunguna yadda likita ya umarta, rage damuwa, motsa jiki, cin abinci mai kyau da kuma guje wa taba da vape na daga cikin matakan da za su taimaka wajen kula da lafiyar zuciya da jijiyoyin jini.
Idan kana da wata matsalar lafiya ko kana shan magunguna, yana da kyau ka tuntubi ƙwararren ma’aikacin lafiya kafin yin wani babban sauyi a tsarin maganinka ko abincinka.




