Masana sun yi gargadi kan amfani da man gyada ko yawu a matsayin man shafawa lokacin jima'i
Daga Wakiliya
Wani babban jami’in kula da rigakafin cututtuka na gidauniyar AIDS Healthcare Foundation (AHF), Taofeek Adeleye, ya gargadi ‘yan Najeriya kan amfani da man gyada, man girki da sauran sinadaran mai a matsayin man shafawa yayin jima’i.
Taofeek Adeleye ya ce amfani da man shafawa mai ruwa (water-based lubricant) ya fi aminci, musamman idan ana amfani da kwaroron roba.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Legas, yayin wani taron horas da ‘yan jarida kan amfani da magungunan PrEP wajen kare kai daga kamuwa da cutar HIV, wanda Hukumar Yaki da Cutar Sida ta Najeriya (NACA) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka shirya.
Adeleye ya kuma shawarci mutane su tabbatar da cewa suna amfani da kwaroron roba mai girman da ya dace da su domin rage yiwuwar tsagewarsa ko zamewarsa yayin jima’i.
Ya ce ya kamata maza su kula da yanayin wurin da za su gudanar da jima’i, tare da kauce wa abubuwan da ka iya jefa su cikin hadari.
Game da man shafawa, Taofeek Adeleye ya ce bai kamata a yi amfani da man gyada, man girki ko wasu sinadaran mai tare da kwaroron roba ba.
Ya ce, “Ba za ka iya amfani da man gyada, man kayan lambu ko wasu irin wadannan sinadarai ba. Sai dai ana iya amfani da man shafawa mai ruwa, wanda shi ne abin da ya dace.”
Adeleye ya kuma yi magana kan amfani da yawu a matsayin madadin man shafawa, inda ya ce idan babu man shafawa, bai kamata mutum ya yi amfani da yawu ba.
Ya ce idan mace za ta yi amfani da yau a irin wannan yanayi, ya fi dacewa ta yi amfani da nata domin kauce wa yiwuwar yada wasu cututtuka daga wani mutum.
Mene ne PrEP?
PrEP wata hanya ce ta kariya daga HIV, inda mutanen da ba su dauke da kwayar cutar amma suke iya fuskantar barazanar kamuwa da ita ke amfani da wasu magungunan rigakafin cutar.
Masana kiwon lafiya sun ce idan ana amfani da PrEP yadda ya kamata, yana matukar rage hadarin kamuwa da HIV, amma ba ya kare mutum daga sauran cututtukan da ake iya dauka ta hanyar jima’i.
Saboda haka, kwaroron roba na ci gaba da kasancewa wani muhimmin bangare na hanyoyin kariya daga HIV da sauran cututtukan da ake dauka ta hanyar jima’i.
Hukumar NACA da abokan huldarta na ci gaba da karfafa amfani da hanyoyi daban-daban na kariya, da suka hada da gwajin HIV, amfani da PrEP, kwaroron roba da kuma samun magani ga masu dauke da cutar.
An shirya taron horas da ‘yan jaridar ne domin kara musu fahimta kan PrEP da sauran hanyoyin kariya daga HIV, ta yadda za su rika isar da sahihan bayanai ga jama’a tare da taimakawa wajen rage yada labaran karya da kyamar masu dauke da cutar.




