Ra'ayoyi

“Ba zan kare waɗanda suka jefa jama’a cikin wahala ba” – Matashi Murtala Provost ya ƙi shiga kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu 2027

Murtala ya ce ba zai yi amfani da ƙarfinsa wajen kare mutanen da ya yi zargin cewa manufofinsu ne suka jefa al’umma cikin wahala ba.

Arewa ce tushen matsalar tsaron Najeriya amma mun ƙi fuskantar gaskiya – Shehu Sani

Shehu Sani ya ce a maimakon a duba yadda matsalar ta samo asali da kuma rawar da shugabannin da suka gabata suka taka wajen magance ta, ana ta ɗora alhakin matsalar kan gwamnatocin da ke kan mulki.

Ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka kafa APC ya ce sun yi kuskure, ya roƙi Allah Ya yafe musu

Jalal, wanda a yanzu yake cikin jam’iyyar adawa, na daga cikin masu fafutukar adawa da gwamnatin APC a matakin jiha da tarayya, yayin da ake tunkarar zaɓen 2027 suna da burin kawar da APC daga sama har ƙasa.

Janar Christopher Musa ya buɗe Ƙudan Zuma: Yanzu dole ya shirya buɗe kundin tarihi

Janar Martin Luther Agwai, ɗan Kudancin Kaduna kuma tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa da Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, ya yi bayani kan tarihin rikice-rikicen yankin. Akwai rikicin Kafanchan na 1987, Zangon Kataf na 1992, rikicin Shari’a na 2000 da kuma rikicin bayan zaɓen 2011.

“Mutanena” Ko Siyasa? – Tambayoyin Da Ya Kamata Christopher Musa Ya Amsa Wa ’Yan Kudancin Kaduna Domin Su Gane Soyayya Ce Ko Kuma Neman...

Yan Kudancin Kaduna, a tsawon shekarun da Honourable Christopher Musa ya kwashe yana aikin soja, wane irin ci gaba ya kawo muku da za ku iya dubawa a yau ku ce: “Eh, wannan mutum ya nuna mana ƙauna da gaske”?

Tudun Biri, Sokoto Da Zurmi: An Kai Hare-Hare Kan Musulmi A Lokacin Musa da aka ce bisa kuskure ne, Amma Babu Wanda Ya Zarge...

Tudun Biri, Sokoto Da Zurmi: An Kai Hare-Hare Kan Musulmi A Lokacin Musa da aka ce bisa kuskure ne, Amma Babu Wanda Ya Zarge Shi Da Yunƙurin Kawar Da Musulmi

Gaskiya Ko Siyasa? Tambayar Da Ya Kamata Ministan Tsaro Ya Amsa – Me El-Rufai Ya Hana Sojoji Yi A Kudancin Kaduna?

El-Rufai ya nemi a naɗa Musa Shugaban Sojin Kasa, Chief of Army Staff (COAS), amma daga baya Tinubu ya naɗa shi Shugaban Hafsoshin Tsaro, Chief of Defence Staff (CDS).

Wani ɗan gwagwarmaya a Kano ya yi alkawarin Naira miliyan ɗaya ga duk wanda ya kawo hujjar amfanin cire tallafin mai ga Talakan Najeriya 

Dr Abdulhamid ya ce yanzu mutane ba sa gamsuwa da taken siyasa da waƙoƙin kamfen kawai, inda ya ƙara da cewa dole ne gwamnati ta nuna abin da ta yi da zai sa jama'a su sake zaɓenta a 2027.

RA’AYIN WAKILIYA | Ba duk mai saka Alƙur’ani a status ba ne munafuki – amma wannan bidiyon ya fallasa wata sabuwar matsalar tarbiyya

Wayar hannu tana iya daukar sakanni kaɗan wajen yin rikodin abin da mutum zai yi nadama a kansa tsawon rayuwarsa. Kafafen sada zumunta kuma ba sa manta komai cikin sauki.

Kwankwaso ya fara nadamar matakin da ya ɗauka na komawa NDC -Bashir Ahmad

A cewarsa, wannan mataki na siyasa ya janyo wa Kwankwaso asarar tasirin siyasar da ya taɓa samu a Jihar Kano, inda ya kasance yana da gagarumin karfin siyasa, amma yanzu ba bu.
- Advertisement -spot_img

DA DUMI-DUMI

An kashe mutumin da ake zargi ya daba wa limamin Juma’a a Wuka a Sokoto

Rahotanni sun ce matashin, wanda aka bayyana da suna Mai Barewa, yana cikin masu ibadar da suka halarci sallar, kuma ya kai wa malamin hari har sau biyu.
- Advertisement -spot_img