Ɗalibin Jami’ar Babcock (Daga Maiduguri) da ya samu First Class ya ce ChatGPT da Gemini sun taimaka masa fahimtar darussan da suka yi masa wahala
Daga Wakiliya
Wani matashi ɗan Najeriya, da ya taso a Maiduguri jihar Borno, Oluwadamilola Soji-Oderinde, ya ce amfani da manhajojin ƙirƙirarriyar basira, ciki har da ChatGPT da Gemini, ya taimaka masa wajen fahimtar darussan da suka yi masa wahala a jami’a.
Matashin mai shekara 20 ya kammala karatun Software Engineering a Jami’ar Babcock da maki 4.52 cikin 5, inda ya samu First Class a digirinsa na farko.
A wata hira da jaridar The Punch, Oluwadamilola ya ce ya yi amfani da manhajojin AI wajen samar da tambayoyin gwaji, tattaunawa kan bayanan karatu da kuma neman karin bayani kan darussan da bai fahimta ba.
Ya ce ɗaya daga cikin darussan da ya fi samun wahalar fahimta shi ne Z Schemas, daga cikin darasin Formal Methods and Specifications, amma AI ta taimaka masa wajen fahimtar sa.
Matashin, wanda ya girma a Maiduguri, ya ce ya fara ɗaukar burin kammala karatu da digiri na farko da muhimmanci a shekararsa ta uku.
Ya ce ya ƙara lokacin karatu, ya riƙa amfani da tambayoyin jarabawar baya, kuma yana neman taimakon abokan karatunsa idan ya samu matsala.
Ya ce yanzu yana son ci gaba da aiki a fannin software engineering da developer relations, tare da gina wata sabuwar kafa da za ta sauƙaƙa wa ’yan Najeriya amfani da manhajojin AI.




