Ma’aikatan Gwamnati sun nemi Tinubu ya dawo da tallafin man fetur saboda tsadar rayuwa
Daga Wakiliya
Gamayyar Haɗakar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dawo da tallafin man fetur, tare da samar da wani alawus na dindindin na tsadar rayuwa (COLA) ga ma’aikatan tarayya domin rage musu radadin hauhawar farashin kayayyaki.
Kiran na kunshe ne cikin wata takardar bukatu mai taken “Federal Workers Charter of Demands”, wadda mai gudanar da kungiyar, Andrew Emelieze, ya sanya wa hannu.
Ma’aikatan sun kuma bukaci gwamnati ta fara biyan kashi 40 na alawus na musamman da kuma duk basussukan da suka taso tun bayan fara aiki da sabon mafi ƙarancin albashi a watan Yulin 2024.
Sun kuma nemi a biya ma’aikata sauran basussukan albashi, musamman na ƙarin girma da aka samu, tare da biyan dukkan bashin fansho da wadanda suka yi ritaya suke bin gwamnati.
Kungiyar ta kuma bukaci gwamnati ta samar da tsarin tallafin iyalai ga ma’aikata, inshorar lafiya ga ma’aikata da ‘yan fansho, da kuma rage harajin da ake cirewa daga alawus-alawus.
Haka kuma, sun nemi gwamnati ta dauki matakan rage farashin kayan masarufi, musamman siminti, ta hanyar kara samar da kayayyakin bukatun yau da kullum a cikin gida domin samar da ayyukan yi.
A bangaren jin dadin jama’a, ma’aikatan sun nemi a samar da tsarin tallafi ga marasa aikin yi da masu karamin karfi, tare da samar da kulawar lafiya kyauta ga yara, mata masu juna biyu da tsofaffi a asibitocin gwamnati.
Sun kuma yi kira ga gwamnati da ta kawo karshen matsalar tsaro tare da tabbatar da sakin mutanen da aka sace a fadin kasar.
Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta cire tallafin man fetur ne a ranar 29 ga Mayun 2023, lamarin da ya jawo karin farashin man fetur da kuma tashin farashin sufuri da sauran kayayyaki.




