Labarai

Da Tinubu ya so APC ta ci zaɓen Osun ko ta halin ƙa-ƙa, da ni za a tura jihar -Wike

Ya ce: “Da Shugaban kasa na son cin zaben Osun da ko-ta-halin ƙa-ƙa, da na je can, kuma da mun ci zaben. Babu abin da gwamnan zai iya yi.”

APC ta zargi an yi mata magudin zaɓe a Osun, ta nemi a sake duba sakamakon

Sai dai APC ta ce tana ci gaba da duba sakamakon da yadda aka gudanar da zaɓen, wanda zai iya zama matakin farko na ƙalubalantar sakamakon da aka sanar.

Wike ya umarci a rushe duk gidajen da suka toshe hanyoyin ruwa a Abuja

Wike ya umarci rushe gidajen da aka gina kan hanyoyin ruwa a Abuja Daga Wakiliya  Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya umarci hukumomin birnin da su fara rushe gidajen da aka gina ko kuma suka tare hanyoyin ruwa a Abuja. Wike ya bayar da umarnin ne bayan ya duba wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a Maitama ranar Talata. Ya ce za a fara aikin nan take kuma za ayi ta aikin har zuwa ranar Asabar, ba tare da la'akari da masu gidajen ba. Ministan ya ce wasu daga cikin gine-ginen mallakin 'yan majalisa da wasu masu hannu da shuni ne, amma doka za ta shafi kowa. Ya ce gine-gine a kan hanyoyin ruwa, toshe magudanan ruwa da zubar da shara na daga cikin abubuwan da ke haddasa ambaliyar ruwa a Abuja. Wike ya kuma umarci hukumomin FCT da su gaggauta kwashe laka da datti daga magudanan ruwa a babban birnin,  Ya ce sauyin yanayi da yawan ruwan sama na taka rawa wajen ambaliyar, amma ayyukan mutane ma na kara tsananta matsalar. Ministan ya ce ba za a dakatar da rushe-rushen saboda ana cikin lokacin siyasa ba, yana mai cewa gwamnati na da niyyar tabbatar da dokokin tsara birnin.

Daga yanzu ‘Daukar doka a hannu’ daidai yake da kisan kai — IGP Disu ya gargadi ’yan Najeriya

Ya gargadi mutanen da ke shirya ko tunzura jama'a, wadanda ke daukar hotuna ko bidiyon abin da ke faruwa su yada shi, da kuma wadanda ke hana ’yan sanda shiga tsakani ko kai agajin gaggawa kan wanda ake zargi, cewa su ma za su iya fuskantar tuhuma.

Adeleke ya sake lashe zaben gwamnan Osun, ya doke Oyebamiji

Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 511,067, inda ya doke dan takarar APC, Bola Oyebamiji, wanda ya samu kuri’u 444,815.

Matafiya A Kula: Hanyar Abuja – Kaduna ta toshe gaba ɗaya a daren nan

Masu tafiya zuwa Abuja ko Kaduna su kula, su kuma yaɗa wannan saƙo domin sauran matafiya su sani 

Zaɓen Osun: Mutum 75 cikin masu zaɓe 342 ne suka kada kuri’a a wata rumfar zabe saboda matsalar BVAS

Wani jami’in INEC da ke aikin zaɓen a rumfar ya tabbatar da samun jinkirin, yana mai cewa ana ƙoƙarin magance matsalar na’urar tare da ci gaba da tantance masu zaɓen da ba su samu damar kammala aikin ba.

Ana cece-kuce bayan nada wata lauya Musulma a matsayin Alkaliyar kotu a Amurka

Hukumar garin Benoit ma ta tabbatar da cewa Ali ta cika sharuddan da dokar Mississippi ta tanada domin zama alkalin kotun karamar hukuma, tana mai cewa kasancewar mutum Musulmi ba ya hana shi rike irin wannan mukami.

ICPC ta gano jami’in da ya saka ‘yan uwansa 14 a albashin gwamnati, da kuma mai karbar albashi 13 shi kadai

Musa Aliyu ya ce hukumar za ta kara amfani da fasaha da bayanai wajen dakile cin hanci da kare dukiyar gwamnati, tare da mayar da hankali kan hana barna kafin faruwar ta.

Beli kyauta ne’ Idan aka nemi ku bayar da kudi, ku kira IGP’ — Rundunar ‘yan Sandan Najeriya

“Doka ba ta ba da damar wani ya biya kudi domin beli ba a kowane ofishin ‘yan sanda a Najeriya,” in ji shi.
- Advertisement -spot_img

DA DUMI-DUMI

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img