Da Tinubu ya so APC ta ci zaɓen Osun ko ta halin ƙa-ƙa, da ni za a tura jihar
Daga Wakiliya
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce da Shugaba Bola Tinubu na son jam’iyyar APC ta lashe zaben gwamnan Osun ko ta halin-ƙa-ƙa, da ya je jihar domin taimaka mata ta samu nasara.
Wike ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da yake magana da ’yan jarida a Abuja, bayan duba wasu wuraren da ambaliyar ruwa ta ci a Maitama.
Da yake magana kan sakamakon zaben da Gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya lashe, Wike ya ce APC za ta iya samun nasara idan Shugaba Tinubu ya kuduri aniyar ganin ta yi nasara ko ta halin kaka.
Ya ce: “Da Shugaban kasa na son cin zaben Osun da ko-ta-halin ƙa-ƙa, da na je can, kuma da mun ci zaben. Babu abin da gwamnan zai iya yi.”
Nyesom Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Rivers ne, ya kasance cikin ’yan PDP da ke goyon bayan Bola Tinubu tun bayan zaben shugaban kasa na 2023, duk da cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP.
An nada Wike Ministan Abuja a gwamnatin Bola Tinubu, wadda jam’iyyar APC ke jagoranta.




