Zaɓen Osun: Mutum 75 cikin masu zaɓe 342 ne suka kada kuri’a a wata rumfar zabe saboda matsalar BVAS
Daga Wakiliya
Masu kaɗa kuri’a a rumfar zaɓe ta Ojude Ala da ke yankin rajista na Iperin, a ƙaramar hukumar Ila ta Jihar Osun, sun koka kan jinkirin kaɗa kuri’a sakamakon matsalar na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS.
Rahotanni sun ce rumfar na da masu zaɓe 342 da aka yi wa rajista.
Sai dai ya zuwa ƙarfe 12:40 na rana, mutum 75 ne kawai aka tantance kuma suka kada kuri’arsu, lamarin da ke nufin kusan kashi 22 cikin 100 na masu rajistar ne suka samu damar kaɗa kuri’a.
Fiye da mutum 260 kuma na ci gaba da jiran a tantance su.
Wani mamba na ƙungiyar ma’aikatan sufuri ta ƙasa, NURTW, Comrade Olaniyan Bamiduro, ya ce na’urar BVAS ta samu matsala sau uku tun bayan fara tantance masu zaɓe.
Ya ce da ba don matsalar na’urar ba, da tuni an tantance mafi yawan masu zaɓen da ke wurin.
Wani jami’in INEC da ke aikin zaɓen a rumfar ya tabbatar da samun jinkirin, yana mai cewa ana ƙoƙarin magance matsalar na’urar tare da ci gaba da tantance masu zaɓen da ba su samu damar kammala aikin ba.
Masu zaɓen sun ci gaba da zama a rumfar, suna jiran a shawo kan matsalar domin su samu damar kaɗa kuri’unsu.




