ICPC ta gano jami'in da ya saka ‘yan uwansa 14 a albashin gwamnati, da kuma mai karbar albashi 13 shi kadai
Daga Wakiliya
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (ICPC) ta ce ta gano wasu mutane da ake zargi da kirkirar ma’aikatan bogi a cikin tsarin biyan albashin gwamnati.
Shugaban hukumar, Musa Aliyu, ya ce an gano wani jami’i da ya saka sunayen ‘yan uwansa 14 cikin tsarin albashi, yayin da wani kuma ake zargi ya rika karbar albashi 13 daban-daban.
Musa Aliyu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taro da kamfanin Image Merchants Promotions Limited ya shirya kan harkokin tattalin arziki da sadarwar gwamnati.
Ya ce binciken hukumar ya gano yadda wasu mutane ke amfani da gibi a tsarin gwamnati domin karbar kudaden da ba su dace ba.
“Mun gano mutum daya da ya saka mutane 14 daga cikin iyalansa a tsarin albashi. Yana zaune a wani otel na gwamnati yana karbar albashi,” in ji shugaban ICPC.
Ya kara da cewa an gano wani mutum da ya saka matarsa, dansa, diyarsa da wasu ‘yan uwa, inda yake karbar albashi 13.
Hukumar ta ce ta gano kusan ma’aikatan bogi 900, kuma ta wallafa sunayensu domin su tabbatar da cewa su ma’aikatan gwamnati ne na gaskiya.
Musa Aliyu ya ce ICPC ta shafe shekara guda tana binciken lamarin, inda ta gano dabarun da ake amfani da su wajen shigar da sunayen mutanen da ba sa aiki cikin jerin ma’aikata.
Ya bayyana cewa a wasu lokuta ana samun sunan mutum a cikin tsarin albashi tare da adireshin imel dinsa, amma idan aka duba asusun banki sai a ga na wani mutum daban.
Shugaban ICPC ya gargadi cewa matsalar ma’aikatan bogi ba ta tsaya kan albashi kadai ba, domin tana iya haifar da biyan kudin fansho, gidaje, inshorar lafiya da sauran alawus-alawus ga mutanen da ba su cancanta ba.
Ya ce a shekarar 2024 hukumar ta samu nasarar gano tare da dawo da sama da naira biliyan 24 na kudaden fanshon ma’aikatan bogi.
Musa Aliyu ya ce hukumar za ta kara amfani da fasaha da bayanai wajen dakile cin hanci da kare dukiyar gwamnati, tare da mayar da hankali kan hana barna kafin faruwar ta.
A nasa bangaren, shugaban kamfanin IMPR, Yusha’u Shuaib, ya ce taron an shirya shi ne domin karfafa gaskiya, rikon amana da inganta sadarwa tsakanin gwamnati da jama’a.





