Jama’a sun fusata bayan an nada wata lauya Musulma a matsayin Alkaliyar kotu a Amurka
Daga Wakiliya
An samu cece-kuce a Amurka bayan an nada wata lauya ‘yar asalin Yemen, Assma Ali, a matsayin alkaliyar kotun karamar hukuma ta Benoit, wani karamin gari da ke jihar Mississippi.
An nada Ali, wadda take sanya hijabi, a matsayin alkalin kotun ne a ranar 5 ga watan Agustan 2026, bayan hukumar da ke tafiyar da garin ta amince da nadin nata.
Ali, wadda aka haifa a Amurka, lauya ce mai kula da harkokin shige da fice, kuma tana gudanar da ofishinta na lauya a Ridgeland, Mississippi.
Ta kammala karatun shari’a a Mississippi College School of Law a shekarar 2017, kuma an ba ta lasisin aikin lauya a Mississippi a wannan shekarar. Tana da kusan shekaru 10 tana aikin lauya.
Bayan nadin nata, wasu masu amfani da kafafen sada zumunta da wasu ‘yan siyasa a Mississippi sun soki nadin, musamman saboda addininta da kuma hijabin da take sanyawa.
Wasu daga cikin masu sukar sun zarge ta da tsatssauran ra’ayoyin tare da ikirarin cewa za ta yi amfani da dokar Musulunci a kotu, amma babu wata hujja da aka gabatar da ke tabbatar da wadannan zarge-zargen.
Ali ta ce za ta gudanar da aikinta cikin adalci da gaskiya, tare da mutunta kundin tsarin mulkin Amurka da dokokin jihar Mississippi.
Wani farfesa a fannin shari’a kuma lauya, Frank Rosenblatt, wanda ya dade da sanin Ali, ya kare ta, yana mai cewa ta cancanci mukamin kuma tana da kyakkyawan matsayi a tsakanin al’ummar lauyoyi.
Ya ce kundin tsarin mulkin Amurka da na Mississippi ba su amince a hana mutum mukamin gwamnati saboda addininsa ba.
Hukumar garin Benoit ma ta tabbatar da cewa Ali ta cika sharuddan da dokar Mississippi ta tanada domin zama alkalin kotun karamar hukuma, tana mai cewa kasancewar mutum Musulmi ba ya hana shi rike irin wannan mukami.
A Amurka, alkalan irin wadannan kotunan kananan hukumomi ana nada su ne domin sauraron laifukan da suka shafi dokokin kananan hukumomi da wasu kananan laifuka, ba alkalan kotunan jiha ba ne.
Nadin Ali ya kuma janyo barazana da cin mutunci a kafafen sada zumunta da kuma ga ofishinta, yayin da wasu kungiyoyi da masu fafutukar kare hakkin dan Adam suka yi Allah-wadai da hare-haren da ake mata saboda addininta.




