Daga Wakiliya
Beli kyauta ne a ofishin ‘yan sanda — CSP Aniete Iniedu
Wani babban jami’in ‘yan sandan Najeriya, CSP Aniete Iniedu, ya ce beli kyauta ne a dukkan ofisoshin ‘yan sanda a kasar, yana mai gargadin cewa babu wata doka da ta bai wa jami’ai damar karbar kudi kafin bayar da beli.
CSP Iniedu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da mai gabatar da shirye-shirye, Nedu, inda ya ce mutane da dama kan sanya hannu a takardun beli ba tare da karanta abin da ke ciki ba.
Ya ce a cikin takardar belin ana bayyana cewa ba a biya ko sisi ba domin samun belin, amma wasu mutane kan yi gaggawar sanya hannu saboda kawai suna son fita daga ofsihin ‘yan sanda.
“Doka ba ta ba da damar wani ya biya kudi domin beli ba a kowane ofishin ‘yan sanda a Najeriya,” in ji shi.
Jami’in ya shawarci duk wanda jami’in ‘yan sanda ya nemi kudi daga gare shi domin beli da ya fita daga Ofishin cikin natsuwa ya kira Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP).
Ya kuma bayyana cewa jama’a za su iya kai korafi ta wadannan hanyoyi:
📞 08057000001
📞 08057000002
📱 08057000003 (WhatsApp/Text)
CSP Aniete Iniedu ya bukaci jama’a su rika kai rahoton duk wani jami’in da ya nemi kudi domin beli, yana mai jaddada cewa beli kyauta ne a karkashin dokar Najeriya.




