An kashe mutumin da ake zargi ya daba wa limamin Juma’a a Wuka a Sokoto
Daga Wakiliya
An kashe wani matashi da ake zargi da daba wa wani malamin addinin Musulunci, Malam Musa Lukwa, wuƙa a wuya, jim kaɗan bayan idar da sallar Juma’a a masallacinsa da ke unguwar Mabera, a birnin Sokoto.
Rahotanni sun ce matashin, wanda aka bayyana da suna Mai Barewa, yana cikin masu ibadar da suka halarci sallar, kuma ya kai wa malamin hari har sau biyu.
Masu ibadar sun yi nasarar cafke wanda ake zargin, inda suka lakada masa duka har ya mutu.
An ce harin na da alaƙa da wani wa’azi da Malam Lukwa ya taɓa yi da ya shafi iyayen Annabi S.A.W, wanda wasu malamai masu alaƙa da ɗariƙa suka nuna ɓacin ransu.
Kafin faruwar lamarin, an ce wanda ake zargin ya taɓa yin barazanar kashe malamin da babban ɗalibinsa, Malam Murtala Assada. An kuma kai rahoton barazanar ga ’yan sanda, lamarin da ya kai ga kama shi da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.
Kakakin rundunar ’yan sandan Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da harin, yana mai cewa Malam Lukwa na karɓar magani a Asibitin Kwararru na Sokoto.
Ya ce wanda ake zargin ya mutu bayan mabiyan malamin sun far masa, yayin da ba a kama kowa ba dangane da kisan.
Rundunar ta ce ta ɗauki matakan hana lamarin ƙara ta’azzara, tare da gudanar da bincike domin gano cikakken abin da ya faru da kuma waɗanda ke da hannu.




