Adeleke ya sake lashe zaben gwamnan Osun, ya doke Oyebamiji

Daga Wakiliya

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a shekarar 2026.

Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 511,067, inda ya doke dan takarar APC, Bola Oyebamiji, wanda ya samu kuri’u 444,815.

Dan takarar ADC ya samu kuri’u 17,180.

A cewar sakamakon karshe da aka sanar, an yi wa masu kada kuri’a 2,339,544 rajista, yayin da aka tantance 1,010,684 daga cikinsu.

Jimillar kuri’un da aka kada ta kai 1,005,800, yayin da kuri’u 20,721 aka soke.

An sanya hannu tare da hatimce sakamakon da jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Joshua Olalekan Ogunwole.

Wannan nasara ta bai wa Ademola Adeleke damar ci gaba da jagorantar jihar Osun a wa’adinsa na biyu.

DA DUMI-DUMI

Rayuwar Alkali Bunza a Hannun Masu Garkuwa: Ya Ce Ya Yi Tafiyar Kilomita 25 Ba Takalmi

Ya kuma ce abin da ya faru da shi ya kara tabbatar masa da bukatar gwamnati ta magance matsalolin talauci, rashin aikin yi da karancin ilimi, wadanda ya ce suna taimakawa wajen yaduwar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

“Ashe ’Yan Arewa Mutanen Kirki Ne Haka?” – Inyamura Ta Yi Mamaki Bayan Direban Keke Ya Mayar Mata da Wayarta da Ta Manta

Chioma ta ce abin ya matukar burge ta, musamman da ta gano cewa Mohammed bai taba mallakar ko amfani da wayar Android ba, amma duk da haka ya mayar da wayar da ta fada hannunsa

Matafiya A Kula: Hanyar Abuja – Kaduna ta toshe gaba ɗaya a daren nan

Masu tafiya zuwa Abuja ko Kaduna su kula, su kuma yaɗa wannan saƙo domin sauran matafiya su sani 

Bayani Dalla-dalla yadda za ku yi rajistar sunan kasuwancin ku a CAC Kyauta

Kada ka biya kowa kuɗi domin wannan rajista. Gwamnati ta ce CAC ba za ta karɓi kuɗin rajistar wannan shirin ba. Haka kuma, ka yi hattara da masu damfara da ke cewa za su gaggauta maka rajista idan ka biya su kuɗi.

Abubuwa 6 da ya kamata a yi kafin ƙarfe 9 na safe domin rage haɗarin shanyewar ɓarin jiki

Shan magunguna yadda likita ya umarta, rage damuwa, motsa jiki, cin abinci mai kyau da kuma guje wa taba da vape na daga cikin matakan da za su taimaka wajen kula da lafiyar zuciya da jijiyoyin jini.

Kanun Labarai

Zaɓen Osun: Mutum 75 cikin masu zaɓe 342 ne suka kada kuri’a a wata rumfar zabe saboda matsalar BVAS

Wani jami’in INEC da ke aikin zaɓen a rumfar ya tabbatar da samun jinkirin, yana mai cewa ana ƙoƙarin magance matsalar na’urar tare da ci gaba da tantance masu zaɓen da ba su samu damar kammala aikin ba.

Adam A. Zango ya sake aure a Jamhuriyar Nijar – Ya Auri Mamah

Adam A. Zango ya sake aure a Jamhuriyar Nijar...

An kama wata Amarya bisa zargin sanya wa mijinta guba kwana 40 da aurensu a Bauchi

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 12 ga watan Agustan 2026, da misalin karfe 3:15 na rana a kauyen Gwamma da ke karamar hukumar Bauchi.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img