Daga yanzu ‘Daukar doka a hannu’ daidai yake da kisan kai — IGP Disu ya gargadi ’yan Najeriya

Daga yanzu ‘Daukar doka a hannu’ kisan kai ne — IGP Disu ya gargadi ’yan Najeriya

Daga Wakiliya

Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, IGP Tunde Disu, ya gargadi ’yan Najeriya kan daukar doka a hannu, yana mai cewa duk wanda ya kai wa wanda ake zargi hari ko ya kashe shi ta hanyar yi wa wanda ake zargin taron dangi zai fuskanci tuhumar kisan kai.

IGP Tunde Disu ya ce an dauki matakin ne domin dakile karuwar kashe mutane ba bisa ka’ida ba da ake samu a sassan kasar.

A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, IGP Tunde Disu ya ce ya umurci kwamishinonin ’yan sanda na jihohi 36 da kuma Abuja da su dauki duk lamari da ya kai ga kisa a matsayin homicide, tare da gudanar da cikakken bincike.

Ya ce dokokin Najeriya sun tanadi hukunci mai tsauri kan kisan kai, inda ya ambaci Sashe na 319 na Criminal Code da Sashe na 221 na Penal Code.

“Duk wanda ya kai wa wanda ake zargi hari ko ya kashe shi yana da laifin kisan kai,” in ji shi.

IGP Disu ya kuma ce laifin ba zai tsaya kan wadanda suka aikata kisan kai kawai ba.

Ya gargadi mutanen da ke shirya ko tunzura jama'a, wadanda ke daukar hotuna ko bidiyon abin da ke faruwa su yada shi, da kuma wadanda ke hana ’yan sanda shiga tsakani ko kai agajin gaggawa kan wanda ake zargi, cewa su ma za su iya fuskantar tuhuma.

Ya ce Sashe na 516 na Criminal Code ya tanadi hukunci kan hada baki wajen aikata laifi, ciki har da makircin kisan kai.

Gargadin na IGP Tunde Disu ya zo ne a daidai lokacin da ake ta yada wasu bidiyoyin mutane na daukar doka a hannu kan mutanen da ake zargi da aikata laifuka.

Daya daga cikin irin wadannan hare-haren shi ne wanda ya yi sanadin mutuwar Ibrahim Mbaya, wanda aka fi sani da Ibee, wani matashin da ya kammala karatu a Jami’ar Jos. An kai masa hari a Jos bayan zargin cewa ya saci wayar iPhone 12, lamarin da ya kai ga mutuwarsa.

’Yan sanda sun ce an kama wasu mutane dangane da lamarin.

IGP Tunde Disu ya bukaci ’yan Najeriya da su daina daukar doka a hannunsu, su rika mika duk wanda ake zargi da aikata laifi ga jami’an tsaro domin gudanar da bincike da daukar matakin da ya dace.

Ya ce rundunar ’yan sandan Najeriya ba za ta kyale wadanda ke da hannu wajen kashe mutane ta hanyar ‘jungle justice ko daukar doka a hannu’ ba, tare da alkawarin gurfanar da wadanda aka samu da laifi a gaban kotu.

DA DUMI-DUMI

Ya Allah Ka Kare Mu Daga Maza Azzalumai – labarin wata maijego da na gani a asibiti ya girgiza ni

Ta haihu babu ko tsinke na haiuwa daga mijin, ya ki rako ta Asibiti, babu wani nashi kuma ko sisi bai bayar ba, ita ce matar shi ta huɗu, haihuwa na 11, yan uwanta suke komai, tana cikin nakuda ma sai da tayi mashi tuwo kafin ta taho Asibiti....

Fitaccen Jarumin Fim Nicolas Cage Ya Ce Yana Iya Tuna Abin da Ya Faru Tun Yana Cikin Mahaifiyarsa

Masana kimiyya sun ce yawancin mutane ba sa iya tuna abubuwan da suka faru kafin su kai kusan shekara biyu ko uku

Adeleke ya sake lashe zaben gwamnan Osun, ya doke Oyebamiji

Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 511,067, inda ya doke dan takarar APC, Bola Oyebamiji, wanda ya samu kuri’u 444,815.

Rayuwar Alkali Bunza a Hannun Masu Garkuwa: Ya Ce Ya Yi Tafiyar Kilomita 25 Ba Takalmi

Ya kuma ce abin da ya faru da shi ya kara tabbatar masa da bukatar gwamnati ta magance matsalolin talauci, rashin aikin yi da karancin ilimi, wadanda ya ce suna taimakawa wajen yaduwar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

“Ashe ’Yan Arewa Mutanen Kirki Ne Haka?” – Inyamura Ta Yi Mamaki Bayan Direban Keke Ya Mayar Mata da Wayarta da Ta Manta

Chioma ta ce abin ya matukar burge ta, musamman da ta gano cewa Mohammed bai taba mallakar ko amfani da wayar Android ba, amma duk da haka ya mayar da wayar da ta fada hannunsa

Kanun Labarai

Matafiya A Kula: Hanyar Abuja – Kaduna ta toshe gaba ɗaya a daren nan

Masu tafiya zuwa Abuja ko Kaduna su kula, su kuma yaɗa wannan saƙo domin sauran matafiya su sani 

Bayani Dalla-dalla yadda za ku yi rajistar sunan kasuwancin ku a CAC Kyauta

Kada ka biya kowa kuɗi domin wannan rajista. Gwamnati ta ce CAC ba za ta karɓi kuɗin rajistar wannan shirin ba. Haka kuma, ka yi hattara da masu damfara da ke cewa za su gaggauta maka rajista idan ka biya su kuɗi.

Abubuwa 6 da ya kamata a yi kafin ƙarfe 9 na safe domin rage haɗarin shanyewar ɓarin jiki

Shan magunguna yadda likita ya umarta, rage damuwa, motsa jiki, cin abinci mai kyau da kuma guje wa taba da vape na daga cikin matakan da za su taimaka wajen kula da lafiyar zuciya da jijiyoyin jini.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img