An kama mutum biyu bisa zargin kisan mai sharhi Danshagamu a Kano

DA DUMI-DUMI

An kama mutum biyu bisa zargin kisan mai sharhi Danshagamu a Kano

Daga Wakiliya

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan Ibrahim Khalil Danshagamu, wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a kafafen sada zumunta.

An kashe Danshagamu ne a gidansa da ke unguwar Gaida, a Karamar Hukumar Kumbotso ta jihar, a daren Litinin.

Rahotanni sun ce an kai masa hari a gidansa, inda daga baya aka same shi cikin jini, tare da zargin cewa an yanke masa makogaro.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, CSP Abdullahi Kiyawa, ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa daga kungiyar ’yan sa-kai ta Gaida da misalin ƙarfe 11 na daren Litinin.

Ya ce shugaban kungiyar ya sanar da ’yan sanda cewa wasu ’yan daba da ba a san ko su waye ba sun kutsa gidan marigayin da ƙarfi tare da kai masa hari,

A cewar Kiyawa, jami’an sashen ’yan sandan Kumbotso sun isa wurin nan take, sannan suka garzaya da Danshagamu zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano domin samun agajin gaggawa.

Sai dai likitoci sun tabbatar da mutuwarsa bayan isar da shi asibitin.

Kiyawa ya ce bayan umarnin kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, jami’an sashen Kumbotso tare da rundunonin musamman sun fara bincike na musamman akan lamarin.

Ya ce binciken ya kai ga kama wasu mutum biyu da ake zargi da alaƙa da kisan.

A yanzu haka, mutanen biyu suna hannun ’yan sanda kuma ana yi musu tambayoyi, yayin da jami’an ke ci gaba da bincike.

Rundunar ta ce ana kuma gudanar da binciken kwararru da na shaidun laifuka domin gano ainihin abin da ya faru da kuma dalilin kai masa harin.

Kwamishinan ’yan sandan ya bayyana damuwarsa kan kisan tare da mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin.

Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta tabbatar an gano wadanda suka aikata laifin, an kama su sannan an gurfanar da su a gaban kotu kamar yadda doka ta tanada.

Rundunar ta ce bincike kan lamarin na ci gaba, kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zarar an kammala binciken.

A halin yanzu, an kara yawan sintiri da ayyukan tattara bayanan sirri a Gaida da kewayenta domin tabbatar da tsaro da hana sake barkewar tashin hankali.

’Yan sandan sun kuma bukaci mazauna yankin da su kasance cikin taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani bayanin da zai taimaka wajen binciken ga ofishin ’yan sanda mafi kusa ko layukan gaggawa na rundunar.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

An kashe mutumin da ake zargi ya daba wa limamin Juma’a a Wuka a Sokoto

Rahotanni sun ce matashin, wanda aka bayyana da suna Mai Barewa, yana cikin masu ibadar da suka halarci sallar, kuma ya kai wa malamin hari har sau biyu.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img