ICPC ta kori jami’inta kan taimaka wa matar El-Rufai shiga wajensa ba tare da izini ba

DA DUMI-DUMI

ICPC ta kori jami’inta kan taimaka wa matar El-Rufai shiga wajensa ba tare da izini ba

Daga Wakiliya

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, ICPC, ta kori wani jami’in tsaro da ake zargi da taimaka wa Aichatou Assabe El-Rufai, ɗaya daga cikin matan tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, wajen shiga wurin da aka tsare mijinta ba tare da izini ba.

Jami’in, mai suna Daniel Stephen, na cikin tawagar tsaron cikin gida ta hukumar.

Rahotanni sun ce an kama shi a kyamarar CCTV yayin da yake taimaka wa matar tsohon gwamnan shiga harabar hukumar a ranar 5 ga Yuli, 2026, ba tare da bin tsarin da aka tanada na karɓar baƙi ba.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa Stephen ya amince da hannunsa cewa ya taimaka wa matar El-Rufai shiga harabar hukumar ta wata ƙofar baya.

A cikin jawabin karbar laifi da ya rubuta da hannunsa a gaban kwamitin bincike, jami’in ya ce ya ɗauki Assabe da mota zuwa harabar hukumar, sannan ya bi da ita ta ƙofar baya zuwa benen da ake tsare da El-Rufai.

Wani jami’in ICPC da aka ambata a rahoton ya ce a yayin ziyarar, Assabe ta miƙa wa mijinta wata takarda, sannan ta ɗauki wata jaka baƙa, inda suka tattauna cikin harshen Hausa kan wani batu da ya shafi shari’a.

Rahoton ya ce ziyarar ta ɗauki kusan mintuna 15, kafin Stephen ya sake raka matar ta fita ta ƙofar bayan, sannan ya kaita da mota zuwa wajen hukumar.

 

Ya amince ya karya dokar hukumar

Stephen ya shaida wa kwamitin binciken cewa yana sane da cewa ziyarar ba ta bi tsarin tsaron hukumar ba.

Ya ce duk wani baƙo da zai shiga harabar ICPC dole ne a rubuta bayanansa a ƙofar shiga sannan ya samu izinin shugaban sashen tsaro kafin a bar shi ya shiga.

A cewar rahoton, jami’in ya amince cewa abin da ya yi ya saɓa wa dokokin hukumar.

 

Zargin taimaka wa wani ɗan uwan El-Rufai

Wasu jami’an ICPC da aka ambata a rahoton sun kuma yi zargin cewa taimakon da Stephen ya yi wa Assabe bai tsaya kan abin da ya faru a ranar 5 ga Yuli ba.

An ce Stephen ya bayyana wani abin da ya faru a baya, inda ya taimaka wa Assabe ta shiga cikin harabar hukumar yayin da jami’ai ke ƙoƙarin tantance ko tana da izinin shiga.

 

Bayan haka, a cewar bayaninsa, wani mutum ya tunkare shi ya bayyana kansa a matsayin ɗan’uwan El-Rufai.

Rahoton ya ce Stephen ya amince ya taimaka wa mutumin, inda ya shigar da shi cikin harabar hukumar ta ƙofar baya.

Ba a bayyana ƙarin bayani kan abin da ya faru da mutumin ko ko an ɗauki wani mataki a kansa ba.

Haka kuma, rahoton bai bayyana martanin Aichatou Assabe El-Rufai ko Nasir El-Rufai kan zarge-zargen ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

An kashe mutumin da ake zargi ya daba wa limamin Juma’a a Wuka a Sokoto

Rahotanni sun ce matashin, wanda aka bayyana da suna Mai Barewa, yana cikin masu ibadar da suka halarci sallar, kuma ya kai wa malamin hari har sau biyu.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img