Labarai

Zan yi aiki tukuru don ganin Tinubu ya zarce a 2027 –  Christopher Musa ya karɓi naɗin da APC ta yi masa

Janar Christopher Musa ya kuma yi kira ga ’yan jam’iyyar APC da sauran ’yan Najeriya masu kishin ƙasa da su kasance cikin haɗin kai, yana mai cewa yana da yakinin APC za ta yi nasara a zaɓen 2027 tare da ci gaba da inganta shugabanci da tsaro a ƙasar.

Tinubu Zai Ci Zabe Kuma APC za ta ci gaba da mulkar Najeriya har bayan 2031 -inji Yari 

Yari ya ce duk da kalubalen da gwamnatin Tinubu ke fuskanta, yana ganin ayyukan gwamnatin cikin shekaru uku da suka gabata za su taimaka wa APC wajen samun ƙarin wa’adi.

Kamfanin Dangote ya faɗaɗa kai man fetur kyauta zuwa Kano da wasu jihohi domin saukar da farashin man a gidajen mai

Ana sa ran rage kuɗin safarar man fetur zai ba ‘yan kasuwa ƙarin damar sauke farashin man a gidajen mai, idan aka samu ci gaba da rage kuɗaɗen da ke cikin tsarin rarraba man.

Maido da Tallafin Man Fetur (Subsidy) zai mayar da Najeriya baya, ya jefa mutane a wahala – Idris

Sai dai ya amince cewa ‘yan Najeriya na fuskantar wahalhalu sakamakon sauye-sauyen, amma ya ce dawo da tallafin man fetur ba mafita ba ce.

1 cikin 4 na mazan da aka yiwa Gwajin DNA a Najeriya ba su ne ubannin yaransu ba – Rahoto

Rahoton ya ce maza masu shekaru 41 zuwa sama ne suka fi yawa cikin wadanda suka nemi gwajin, inda suka kai kashi 48 cikin 100.

APC ta bukaci a binciki Dino Melaye da wasu jiga-jigan PDP kan zargin alaka da Dan Damfarar Intanet Hushpuppi

A wata sanarwa da Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Kasa na APC, Yekini Nabena, ya fitar a Abuja ranar Asabar, jam’iyyar ta bukaci Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), da Hukumar Leken Asiri kan Harkokin Kudi ta Najeriya (NFIU), da sauran hukumomi su gudanar da cikakken bincike.

Bankaɗo tsoffin takardun zargin Tinubu na iya bata martabar Najeriya tare da yin tasiri a zaɓen 2027 – Buratai

Bankaɗo takardun tsofaffin laifukan da ake zargin Tinubu ko fitar da su na iya yin illa ga martabar Najeriya a idon duniya, sannan za su iya yin tasiri a zaben 2027 - Buratai ya bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da zarge-zargen

Gwamnatin Tarayya ta kulla yarjejeniyar farfado da Kamfanin Karafa na Delta cikin watanni 18 kan dala biliyan 1.3b$

Ma’aikatar Raya Karafa ta Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da Premium Steel and Mines Limited (PSML) domin farfado da kamfanin karafa na Delta, da ke Ovwian-Aladja a Jihar Delta.

Bai kamata addini ya zama ma’aunin zaɓe a Najeriya ba domin a tsarin dimokuraɗiyya, tikitin Musulmi da Musulmi, Kirista da Kirista, Musulmi da Kirista...

Ya ce da a ce Najeriya tana tafiyar da mulkin Shari’a yadda Alƙur’ani da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) suka tanada, to Musulmi ne kaɗai za su iya neman shugabanci.

Da kyar Tinubu ya amince da Osinbajo a matsayin mataimakin Buhari – ya dage sai an bai wa matarsa Oluremi

Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya kuma ce lokacin da Buhari ya nemi goyon bayansa bayan taron APC na 2014, ya sharɗanta masa cewa kada ya tsaya da tikitin Musulmi da Musulmi.
- Advertisement -spot_img

DA DUMI-DUMI

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img