Wike ya umarci a rushe duk gidajen da suka toshe hanyoyin ruwa a Abuja
Daga Wakiliya
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya umarci hukumomin birnin da su fara rushe gidajen da aka gina ko kuma suka tare hanyoyin ruwa a Abuja.
Wike ya bayar da umarnin ne bayan ya duba wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a Maitama ranar Talata.
Ya ce za a fara aikin nan take kuma za ayi ta aikin har zuwa ranar Asabar, ba tare da la'akari da masu gidajen ba.
Ministan ya ce wasu daga cikin gine-ginen mallakin ‘yan majalisa da wasu masu hannu da shuni ne, amma doka za ta shafi kowa.
Ya ce gine-gine a kan hanyoyin ruwa, toshe magudanan ruwa da zubar da shara na daga cikin abubuwan da ke haddasa ambaliyar ruwa a Abuja.
Wike ya kuma umarci hukumomin FCT da su gaggauta kwashe laka da datti daga magudanan ruwa a babban birnin,
Ya ce sauyin yanayi da yawan ruwan sama na taka rawa wajen ambaliyar, amma ayyukan mutane ma na kara tsananta matsalar.
Ministan ya ce ba za a dakatar da rushe-rushen saboda ana cikin lokacin siyasa ba, yana mai cewa gwamnati na da niyyar tabbatar da dokokin tsara birnin.





