NDC ta buƙaci Talakawa su tara mata gudunmawar Naira dubu ɗai-ɗai (N1,000) don yaƙin neman zaɓen 2027
Daga Wakiliya
Jam’iyyar NDC ta ce za ta nemi tallafin kuɗin yaƙin neman zaɓenta daga talakawan Najeriya, domin rage tasirin attajirai a harkokin siyasar ƙasar.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, ne ya bayyana hakan a shirin Prime Time na Arise News ranar Laraba.
Sanata Dickson, wanda ke wakiltar Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya ce jam’iyyar za ta bai wa ’yan Najeriya damar bayar da gudunmawa daga N1,000 ko N2,000 domin gudanar da ayyukanta.
Ya ce NDC ita ce jam’iyya ɗaya tilo a Najeriya da ba ta karɓar kuɗin gudanar da ayyukanta daga baitulmalin gwamnati.
“Ba za ku bari masu kuɗi da attajirai, waɗanda yanzu suka zama tiriliyoyin kuɗi ta hanyar amfani da albarkatun gwamnati, su riƙa ɗaukar nauyin dimokuraɗiyyarku ba,” in ji shi.
Ya ce tsarin bayar da gudunmawar zai bai wa talakawa da waɗanda ke jin an danne su damar taka rawa wajen tafiyar da jam’iyyar da kuma dimokuraɗiyyar ƙasar.
Sanatan ya kuma bayyana cewa jam’iyyar na ci gaba da tuntubar juna kan waɗanda za su kasance cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, kuma za ta sanar da sunayensu nan ba da jimawa ba.
Ya ce ba sa son maimaita abin da ya ce jam’iyyar da ke mulki ta yi, na fitar da jerin sunaye sannan daga baya ta janye su.
Sanata Dickson ya yi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, da hukumomin tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da an gudanar da zaɓen 2027 cikin ’yanci, adalci da gaskiya.
Ya ce NDC za ta je gaban ’yan Najeriya da manufofinta, kuma za ta fafutukar ganin an kare kowace ƙuri’a.
“Za mu kai batunmu ga ’yan Najeriya, kuma za mu yi yaƙi domin kowace ƙuri’a. Za a kalubalanci kowace ƙuri’a,” in ji shi.




