APC ta bukaci a binciki Dino Melaye da wasu jiga-jigan PDP kan zargin alaka da Dan Damfarar Intanet Hushpuppi

APC ta bukaci a binciki Dino Melaye da wasu jiga-jigan PDP kan zargin alaka da Dan Damfarar Intanet Hushpuppi

Daga Wakiliya

Jam’iyyar APC ta bukaci hukumomin Najeriya su binciki tsohon Sanatan Kogi, Dino Melaye, da wasu manyan jami’an jam’iyyar PDP kan rahotannin da ke alakanta su da dan damfarar intanet, Hushpuppi.

Wata ‘yar jarida mai zaman kanta, Kemi Olunloyo, ce ta bayyana rahotannin da ke cewa wasu manyan ‘yan PDP, ciki har da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, dan takarar PDP na shugaban kasa a 2019, Atiku Abubakar, da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, na da alaka da Hushpuppi.

A wata sanarwa da Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Kasa na APC, Yekini Nabena, ya fitar a Abuja ranar Asabar, jam’iyyar ta bukaci Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), da Hukumar Leken Asiri kan Harkokin Kudi ta Najeriya (NFIU), da sauran hukumomi su gudanar da cikakken bincike.

APC ta ce ya kamata a binciki zarge-zargen da suka shafi safarar kudade da kuma alakarta wasu daga cikin manyan ‘yan PDP da Hushpuppi.

Hushpuppi dai an kama shi a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa, sannan aka mika shi ga hukumomin Amurka domin fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi damfarar intanet da sauran laifukan da suka shafi kudi.

Rahotannin da APC ta ambata sun ce laifukan da ake zargin Hushpuppi da aikatawa sun hada da damfara da kudaden da suka kai daruruwan biliyoyin naira.

DA DUMI-DUMI

Bankaɗo tsoffin takardun zargin Tinubu na iya bata martabar Najeriya tare da yin tasiri a zaɓen 2027 – Buratai

Bankaɗo takardun tsofaffin laifukan da ake zargin Tinubu ko fitar da su na iya yin illa ga martabar Najeriya a idon duniya, sannan za su iya yin tasiri a zaben 2027 - Buratai ya bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da zarge-zargen

Gwamnatin Birtaniya ta bukaci Musulmi su rage amfani da ruwa wajen alwala

Wasu masu fafutukar kare hakkin al'umma sun kuma ce Musulunci kansa ya yi kira da a guji barnatar da ruwa yayin alwala (almubazzaranci haramun ne a musulunci).

Kirista ya shiga Gasar Karatun Alƙur’ani a Masar, ya ci kyautar Umrah ya bai wa maƙwabciyarsa Musulma

Um Ali ta bayyana farin cikinta, inda Mina ya ce ya gan ta tana share hawayen farin ciki bayan ya sanar da ita cewa za ta samu damar zuwa Umrah.

Gwamnatin Tarayya ta kulla yarjejeniyar farfado da Kamfanin Karafa na Delta cikin watanni 18 kan dala biliyan 1.3b$

Ma’aikatar Raya Karafa ta Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da Premium Steel and Mines Limited (PSML) domin farfado da kamfanin karafa na Delta, da ke Ovwian-Aladja a Jihar Delta.

Masana sun yi gargadi kan amfani da man gyada ko yawu a matsayin man shafawa lokacin jima’i

Ya ce, “Ba za ka iya amfani da man gyada, man kayan lambu ko wasu irin wadannan sinadarai ba. Sai dai ana iya amfani da man shafawa mai ruwa, wanda shi ne abin da ya dace.”

Kanun Labarai

Me ya sa za ku saka duk wanda kuka taɓa magana da shi sau ɗaya ko biyu a WhatsApp Group ɗin aurenku? – Mr....

Mr. Abdul Reacts ya ce matasan Najeriya da dama kan taimaka wa akalla biki ɗaya kusan kowane wata, ko da kuwa ba su da hali, abin da ya kwatanta da wani nau'in “haraji” da ake biya saboda kasancewa cikin abokan hulɗa.

Bai kamata addini ya zama ma’aunin zaɓe a Najeriya ba domin a tsarin dimokuraɗiyya, tikitin Musulmi da Musulmi, Kirista da Kirista, Musulmi da Kirista...

Ya ce da a ce Najeriya tana tafiyar da mulkin Shari’a yadda Alƙur’ani da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) suka tanada, to Musulmi ne kaɗai za su iya neman shugabanci.

Tinubu ya bai wa Famadewa ragamar tsara sabon tsarin tsaron Najeriya na shekaru biyar

Shugaban ya ba kwamitin kwanaki 90 domin kammala aikin da gabatar da shi gare shi domin amincewa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img