Bankaɗo takardun tsofaffin laifukan da ake zargin Tinubu ko fitar da su na iya yin illa ga martabar Najeriya a idon duniya, sannan za su iya yin tasiri a zaben 2027 – Buratai ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da zarge-zargen
Daga Wakiliya
Tsohon Shugaban Rundunar Sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da abin da ya kira tsoma bakin kasashen waje cikin harkokin Najeriya.
Buratai ya yi wannan kira ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan yiwuwar fitar da wasu takardu da ake dangantawa da binciken zarge-zargen safarar miyagun kwayoyi da aka yi kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu sama da shekaru 30 da suka gabata.
Wata kotun tarayya a Washington DC ta bai wa Tinubu, FBI da Ma'aikatar Shari'a ta Amurka wa'adin zuwa ranar 28 ga Agusta, 2026, domin su bayyana matsayinsu kan fitar da takardun.
Buratai ya ce batun bai shafi Bola Tinubu kadai ba, yana kuma da alaka da martabar Najeriya da ‘yan kasar sama da miliyan 250.
Ya ce bai kamata a bar wani al'amari da ya faru sama da shekaru 30 da suka gabata ya zama abin da zai ayyana rayuwar siyasar Tinubu ko kuma ya bata sunan Najeriya ba.
Tsohon Shugaban Sojin ya kuma tambayi ko ya dace wata kotun Amurka ta yanke hukunci kan martabar Shugaban Najeriya da aka zaba ta hanyar kuri'ar ‘yan Najeriya.
Buratai ya ce Najeriya na da hukumomi da tsarin dimokuradiyya da ya kamata a bi wajen tambayar shugabanni da kuma neman a yi musu bincike.
Ya kuma yi gargadin cewa fitar da takardun na iya yin illa ga martabar Najeriya a idon duniya, musamman wajen jawo jarin kasashen waje, yawon bude ido, taimakon raya kasa da kuma kudaden da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje ke turawa gida.
Ya ce lokaci na fitar da takardun na iya zama barazana ga nasarar Tinubu, musamman ganin cewa Najeriya na gab da babban zaben 2027.
Buratai ya yi gargadin cewa bai kamata wani mataki daga kasashen waje ya zama sanadin yin tasiri kan zabukan Najeriya ba.
Sai dai ya jaddada cewa matsayinsa ba yana nufin ya kamata a kare shugabanni daga bincike ba ne.
Ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka ta hanyar diflomasiyya, sannan ya shawarci tawagar lauyoyin Tinubu da su yi amfani da dukkan hanyoyin doka da suke da su.
Buratai ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne kare martabar Najeriya da ‘yancinta, ba wai kare wani mutum ko wata jam'iyya ba.
“Wannan ba batun kare Tinubu a matsayin mutum ba ne; batun kare Najeriya ne,” in ji Buratai.




