Maido da Tallafin Man Fetur (Subsidy) zai mayar da Najeriya baya, ya jefa mutane a wahala – Idris
Daga Wakiliya
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce dawo da tallafin man fetur zai mayar da Najeriya baya, tare da ƙara matsin tattalin arziki.
Ya ce cire tallafin ya samar da Naira tiriliyan 15.8 ga tarayyar Najeriya tsakanin Yunin 2023 da Disambar 2025, inda jihohi da ƙananan hukumomi suka samu kaso mai yawa.
A cewar Idris, ƙarin kuɗaɗen sun taimaka wajen biyan albashi da fansho, da kuma gudanar da ayyukan kiwon lafiya, ilimi da gine-gine.
Ya ce sauye-sauyen sun kuma taimaka wajen ƙara hakar mai, jawo masu zuba jari da ƙarfafa ajiyar kuɗaɗen waje.
Sai dai ya amince cewa ‘yan Najeriya na fuskantar wahalhalu sakamakon sauye-sauyen, amma ya ce dawo da tallafin man fetur ba mafita ba ce.
Ministan ya yi kira da a maida hankali wajen ganin amfanin sauye-sauyen ya ƙara bayyana ga ‘yan Najeriya.





