Zan yi aiki tukuru don ganin Tinubu ya zarce a 2027 – Christopher Musa ya karɓi naɗin da APC ta yi masa
Daga Wakiliya
Ministan Tsaro na Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa (ritaya), ya ce zai yi aiki tukuru wajen ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Janar Christopher Musa ya bayyana hakan ne bayan amincewa da naɗin da jam’iyyar APC ta yi masa a matsayin Sakataren Tsaro na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar a 2027.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Leah Katung-Babatunde, ta fitar ranar Litinin, ministan ya ce ya karɓi naɗin ne a matsayin ƙarin nauyin hidima da aka ɗora masa bisa amincewar Shugaba Tinubu da shugabannin jam’iyyar.
Ya ce zai yi amfani da ƙwarewarsa wajen gudanar da ayyukan da aka ɗora masa cikin ƙwazo da bin tsari, domin taimakawa APC samun nasara a zaɓen 2027.
Sai dai Janar Musa ya jaddada cewa, duk da wannan aikin siyasa da zai yi wa jam’iyyar, babban aikinsa na kundin tsarin mulki shi ne kare iyakokin Najeriya da rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa.
“Tsaron ƙasa shi ne babban abin da muka fi ba muhimmanci,” in ji shi.
Ya ce ayyukan sojoji da sauran hukumomin tsaro, da kuma gyare-gyaren da ake yi a fannin tsaro, za su ci gaba da gudana ba tare da katsewa ba.
Janar Christopher Musa ya kuma yi kira ga ’yan jam’iyyar APC da sauran ’yan Najeriya masu kishin ƙasa da su kasance cikin haɗin kai, yana mai cewa yana da yakinin APC za ta yi nasara a zaɓen 2027 tare da ci gaba da inganta shugabanci da tsaro a ƙasar.





